1
Farawa 22:14
Sabon Rai Don Kowa 2020
Ibrahim kuwa ya ba wa wurin suna, UBANGIJI Zai Tanada. Gama kamar yadda ake ce har yă zuwa yau, “A bisan dutsen UBANGIJI, za a tanada.”
Compare
Explore Farawa 22:14
2
Farawa 22:2
Sai Allah ya ce, “Ka ɗauki ɗanka, makaɗaicin ɗanka Ishaku, wanda kake ƙauna, ka tafi yankin Moriya, ka miƙa shi hadaya ta ƙonawa a can a kan ɗaya daga cikin duwatsun da zan nuna maka.”
Explore Farawa 22:2
3
Farawa 22:12
Mala’ikan ya ce, “Kada ka yi wa yaron nan rauni. Kada kuma ka ji masa ciwo. Yanzu na san cewa kana tsoron Allah, gama ba ka hana ni ɗanka, makaɗaicin ɗanka ba.”
Explore Farawa 22:12
4
Farawa 22:8
Ibrahim ya amsa ya ce, “Ɗana, Allah kansa zai tanada ɗan ragon hadayar ƙonawa.” Sai su biyu suka ci gaba da tafiya.
Explore Farawa 22:8
5
Farawa 22:17-18
tabbatacce zan albarkace ka, zan kuma sa zuriyarka su yi yawa kamar taurari a sararin sama, kamar kuma yashi a bakin teku. Zuriyarka za su mallaki biranen abokan gābansu, ta wurin zuriyarka kuma dukan al’umman duniya za su sami albarka, domin ka yi mini biyayya.”
Explore Farawa 22:17-18
6
Farawa 22:1
Bayan abubuwan nan suka faru, sai Allah ya gwada Ibrahim. Ya ce masa, “Ibrahim!” Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga ni.”
Explore Farawa 22:1
7
Farawa 22:11
Amma mala’ikan UBANGIJI ya kira shi daga sama ya ce, “Ibrahim, Ibrahim!” Sai Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga ni.”
Explore Farawa 22:11
8
Farawa 22:15-16
Mala’ikan UBANGIJI ya kira Ibrahim daga sama sau na biyu ya ce, “Na rantse da kaina, in ji UBANGIJI, domin ka yi wannan, ba ka kuwa hana ni ɗanka, makaɗaicin ɗanka ba
Explore Farawa 22:15-16
9
Farawa 22:9
Sa’ad da suka isa wurin da Allah ya faɗa masa, sai Ibrahim ya gina bagade a can, ya kuma shisshirya itacen a kai. Ya ɗaura ɗansa Ishaku, ya kwantar da shi a kan itacen, a bisa bagaden.
Explore Farawa 22:9
Home
Bible
Plans
Videos