1
Farawa 32:28
Sabon Rai Don Kowa 2020
Sai mutumin ya ce, “Sunanka ba zai ƙara zama Yaƙub ba, amma Isra’ila, gama ka yi kokawa da Allah da mutane, ka kuwa yi rinjaye.”
Compare
Explore Farawa 32:28
2
Farawa 32:26
Sa’an nan mutumin ya ce, “Bar ni in tafi, gama gari ya waye.” Amma Yaƙub ya amsa ya ce, “Ba zan bar ka ka tafi ba, sai ka sa mini albarka.”
Explore Farawa 32:26
3
Farawa 32:24
Saboda haka sai aka bar Yaƙub shi kaɗai. Sai ga wani mutum ya zo ya yi kokawa da shi har wayewar gari.
Explore Farawa 32:24
4
Farawa 32:30
Saboda haka Yaƙub ya kira wurin Feniyel, yana cewa, “Domin na ga Allah fuska da fuska, duk da haka aka bar ni da rai.”
Explore Farawa 32:30
5
Farawa 32:25
Da mutumin ya ga cewa bai fi ƙarfin Yaƙub ba, sai ya bugi kwarin ƙashin cinyar Yaƙub, sai gaɓar ƙashin cinyarsa ya goce, a sa’ad da yake kokawa da mutumin.
Explore Farawa 32:25
6
Farawa 32:27
Mutumin ya tambaye shi ya ce, “Mene ne sunanka?” Yaƙub ya amsa ya ce, “Yaƙub.”
Explore Farawa 32:27
7
Farawa 32:29
Yaƙub ya ce, “Ina roƙonka, faɗa mini sunanka.” Amma mutumin ya amsa ya ce, “Me ya sa kake tambayata sunana?” Sa’an nan ya albarkace shi.
Explore Farawa 32:29
8
Farawa 32:10
Ban cancanci dukan alheri da amincin da ka nuna wa bawanka ba. Da sanda kaɗai nake sa’ad da na ƙetare wannan Urdun, amma ga shi yanzu na zama ƙungiyoyi biyu.
Explore Farawa 32:10
9
Farawa 32:32
Wannan ya sa har wa yau Isra’ilawa ba sa cin jijiyar ƙashin cinya wadda take a kwarin ƙashin cinya, domin an taɓa kwarin ƙashin cinyar Yaƙub kusa da jijiyar.
Explore Farawa 32:32
10
Farawa 32:9
Sa’an nan Yaƙub ya yi addu’a, “Ya Allah na mahaifina Ibrahim, Allah na mahaifina Ishaku. Ya UBANGIJI kai da ka ce mini, ‘Koma ƙasarka zuwa wurin danginka, zan kuma sa ka yi albarka.’
Explore Farawa 32:9
11
Farawa 32:11
Ka cece ni, ina roƙonka daga hannun ɗan’uwana Isuwa, gama ina tsoro zai zo yă fāɗa mini, yă karkashe mu duka, ’ya’ya da iyaye.
Explore Farawa 32:11
Home
Bible
Plans
Videos