1
Yohanna 13:34-35
Sabon Rai Don Kowa 2020
“Sabon umarni nake ba ku. Ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, ku ma ku ƙaunaci juna. Ta haka kowa zai san cewa ku almajiraina ne, in kuna ƙaunar juna.”
Compare
Explore Yohanna 13:34-35
2
Yohanna 13:14-15
Da yake ni da nake Ubangijinku da kuma Malaminku, na wanke ƙafafunku, haka ku ma ya kamata ku wanke ƙafafun juna. Na ba ku misali domin ku yi yadda na yi muku.
Explore Yohanna 13:14-15
3
Yohanna 13:7
Yesu ya amsa ya ce, “Yanzu ba ka fahimci abin da nake yi ba, amma nan gaba za ka gane.”
Explore Yohanna 13:7
4
Yohanna 13:16
Gaskiya nake gaya muku, ba bawan da ya fi maigidansa, ko ɗan saƙon da ya fi wanda ya aike shi.
Explore Yohanna 13:16
5
Yohanna 13:17
Yanzu da kuka san waɗannan abubuwa, ku masu albarka ne, in kuka yi su.
Explore Yohanna 13:17
6
Yohanna 13:4-5
saboda haka ya tashi daga cin abincin, ya tuɓe rigarsa ta waje, ya ɗaura tawul a ƙugunsa. Bayan haka, sai ya zuba ruwa a cikin kwano, sa’an nan ya fara wanke ƙafafun almajiransa, yana sharewa da tawul wanda ya ɗaura.
Explore Yohanna 13:4-5
Home
Bible
Plans
Videos