1
Far 45:5
Littafi Mai Tsarki
Yanzu fa, kada ku damu ko kuwa ku ji haushin kanku domin kun sayar da ni a nan, gama Allah ne ya aike ni a gabanku don in ceci rai.
Compare
Explore Far 45:5
2
Far 45:8
Don haka, ba ku kuka aiko ni nan ba, amma Allah ne, shi ne kuwa ya sa in zama uba ga Fir'auna, da shugaban gidansa duka, mai mulki kuma bisa ƙasar Masar duka.
Explore Far 45:8
3
Far 45:7
Allah kuwa ya aike ni a gabanku, domin in cetar muku da ringi a duniya, in kuma rayar muku kuɓutattu masu yawa.
Explore Far 45:7
4
Far 45:4
Yusufu ya ce wa 'yan'uwansa. “Ku matso kusa da ni, ina roƙonku.” Suka matso kusa. Sai ya ce, “Ni ne ɗan'uwanku, Yusufu, wanda kuka sayar zuwa Masar.
Explore Far 45:4
5
Far 45:6
Gama shekara biyu ke nan da ake yunwa a ƙasar, amma da sauran shekara biyar masu zuwa da ba za a yi noma ko girbi ba.
Explore Far 45:6
6
Far 45:3
Yusufu kuwa ya ce wa 'yan'uwansa, “Ni ne Yusufu. Mahaifina yana da rai har yanzu?” Amma 'yan'uwansa ba su iya ba shi amsa ba, gama sun firgita a gabansa.
Explore Far 45:3
Home
Bible
Plans
Videos