Sai ya sa wa Yusufu albarka, ya ce,
“Allah na Ibrahim da Ishaku,
Iyayena da suka yi tafiyarsu a
gabansa,
Allah da ya bi da ni
Dukan raina har wa yau, ya sa musu
albarka.
Mala'ikan da ya fanshe ni
Daga dukan mugunta,
Ya sa wa samarin albarka,
Bari a dinga ambatarsu da sunana,
Da sunan Ibrahim da na Ishaku iyayena,
Bari kuma su riɓaɓɓanya, su zama
taron jama'a a tsakiyar duniya.”