1
Far 50:20
Littafi Mai Tsarki
A nufinku mugunta ce kuka yi mini, amma Allah ya maishe ta alheri, don a rayar da jama'a masu yawa waɗanda suke da rai a yau.
Compare
Explore Far 50:20
2
Far 50:19
Amma Yusufu ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ni ba a matsayin Allah nake ba.
Explore Far 50:19
3
Far 50:21
Don haka kada ku ji tsoro, zan tanada muku, ku da ƙanananku.” Ta haka ya ta'azantar da su, ya yi musu magana ta kwantar da zuciya.
Explore Far 50:21
4
Far 50:17
ya ce, ‘Ku faɗa wa Yusufu, ina roƙonsa, ya gafarta laifin 'yan'uwansa da zunubansu, gama sun yi masa mugunta.’ Yanzu fa, muna roƙonka, ka gafarta laifofin bayin Allah na mahaifinka.” Yusufu ya yi kuka sa'ad da suka yi magana da shi.
Explore Far 50:17
5
Far 50:24
Yusufu kuwa ya ce wa 'yan'uwansa, “Ina gab da mutuwa, amma lalle Allah zai ziyarce ku, zai kuwa haurar da ku daga wannan ƙasa zuwa ƙasar da ya rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.”
Explore Far 50:24
6
Far 50:25
Sa'an nan Yusufu ya rantse wa 'ya'yan Isra'ila da cewa, “Hakika Allah zai ziyarce ku, ku kuma sai ku haura da ƙasusuwana daga nan.”
Explore Far 50:25
7
Far 50:26
Yusufu ya rasu yana da shekara ɗari da goma. Sai suka shafe shi da maganin hana ruɓa. Aka kuwa sa shi a akwatin gawa cikin Masar.
Explore Far 50:26
Home
Bible
Plans
Videos