Sai kuma ya kai shi Urushalima, ya ɗora shi can kan tsororuwar Haikali, ya ce masa, “In dai kai Ɗan Allah ne, to, dira ƙasa daga nan, don a rubuce yake cewa,
“ ‘Zai yi wa mala'ikunsa umarni game da kai, su kiyaye ka,’
da kuma
‘Za su tallafe ka,
Don kada ka yi tuntuɓe da dutse.’ ”
Sai Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai kuwa an ce, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”