YouVersion Logo
Search Icon

Farawa 26

26
Ishaku da Abimelek
1Aka yi yunwa a ƙasar; ban da yunwar da aka yi da fari a zamanin Ibrahim, sai Ishaku ya tafi wurin Abimelek sarkin Filistiyawa a Gerar. 2Ubangiji kuwa ya bayyana ga Ishaku ya ce, “Kada ka gangara zuwa Masar; ka yi zauna a ƙasar da zan faɗa maka. 3Ka zauna a wannan ƙasa na ɗan lokaci, zan kuwa kasance tare da kai, zan kuma albarkace ka. Gama zan ba da waɗannan ƙasashe gare ka da kuma zuriyarka. Zan kuma cika rantsuwar da na yi wa mahaifinka Ibrahim. 4Zan sa zuriyarka ta yi yawa kamar taurari a sararin sama zan kuwa ba su dukan waɗannan ƙasashe, ta wurin ’ya’yanka kuma za a albarkaci dukan al’umman duniya, 5domin Ibrahim ya yi mini biyayya ya kuma kiyaye umarnaina, ƙa’idodina da kuma dokokina.” 6Sai Ishaku ya zauna a Gerar.
7Sa’ad da mutanen wurin suka tambaye shi game da matarsa, sai ya ce, “’Yar’uwata ce,” gama yana tsoro yă ce, “Ita matata ce.” Ya yi tunani, “Mutane wannan wuri za su kashe ni ta dalili Rebeka, domin kyakkyawa ce.”
8Sa’ad da Ishaku ya daɗe a can, sai Abimelek sarkin Filistiyawa ya duba daga taga ya ga Ishaku yana rungumar matarsa Rebeka. 9Saboda haka Abimelek ya aika Ishaku yă je, sa’an nan ya ce, “Tabbatacce ita matarka ce! Me ya sa ka ce, ‘Ita ’yar’uwata ce?’ ”
Ishaku ya amsa masa ya ce, “Don na yi tsammani zan rasa raina saboda ita.”
10Sa’an nan Abimelek ya ce, “Me ke nan ka yi mana? Da a ce wani daga mazanmu ya kwana da matarka, ai, da ka jawo laifi a kanmu.”
11Saboda haka Abimelek ya yi umarni ga dukan mutane. “Duk wanda ya fitine wannan mutum ko matarsa, tabbatacce za a kashe shi.”
12Ishaku ya shuka hatsi a wannan ƙasa, a shekaran nan ya yi girbi ninki ɗari, domin Ubangiji ya albarkace shi. 13Mutumin ya arzuta, arzikinsa ya yi ta haɓaka har ya zama attajiri. 14Ya kasance da garkunan tumaki da na shanu da bayi masu yawa, har Filistiyawa suka yi ƙyashinsa. 15Saboda haka dukan rijiyoyin da bayin mahaifinsa suka haƙa a kwanakin da mahaifinsa Ibrahim yake da rai, Filistiyawa sun toshe su, suka kuma ciccike su da ƙasa.
16Sai Abimelek ya ce wa Ishaku, “Fita daga cikinmu; ka fi ƙarfinmu.”
17Saboda haka Ishaku ya fita daga can, ya yi sansani a Kwarin Gerar, ya kuma zauna a can. 18Ishaku ya sāke tona rijiyoyi waɗanda dā aka haƙa a zamanin Ibrahim mahaifinsa, gama Filistiyawa suka tattoshe bayan mutuwar Ibrahim, ya kuma sa musu sunayen da mahaifinsa ya ba su.
19Barorin Ishaku suka haƙa cikin kwarin suka kuwa sami rijiya mai ruwa mai kyau a can. 20Amma makiyayan Gerar suka yi faɗa da na Ishaku suka ce, “Ruwan namu ne!” Saboda haka Ishaku ya ba wa rijiyar suna Esek,#26.20 Esek yana nufin rikici. domin sun yi faɗa da shi. 21Sai suka haƙa wata rijiya, amma suka yi faɗa a kanta ita ma, saboda haka ya ce da ita Sitna.#26.21 Sitna yana nufin adawa. 22Sai Ishaku ya matsa daga can ya sāke haƙa wata rijiyar, babu wani kuma da yi faɗa a kanta. Sai ya ba ta suna Rehobot,#26.22 Rehobot yana nufin ɗaki. yana cewa, “Yanzu Ubangiji ya ba mu wuri, za mu kuwa yi ta haihuwa a ƙasar.”
23Daga can ya haura zuwa Beyersheba. 24A wannan dare Ubangiji ya bayyana gare shi ya ce, “Ni ne Allah na mahaifinka Ibrahim. Kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai, zan albarkace ka, zan kuma ƙara yawan zuriyarka saboda bawana Ibrahim.”
25Sai Ishaku ya gina bagade a can, ya kuma kira bisa sunan Ubangiji. A can ya kafa tentinsa, a can kuma bayinsa suka haƙa wata rijiya.
26Ana cikin haka, sai Abimelek ya zo wurinsa daga Gerar, tare da Ahuzzat mai ba shi shawara da Fikol shugaban mayaƙansa. 27Ishaku ya tambaye su, “Me ya kawo ku gare ni, da yake kun yi gāba da ni, kuka kuma kore ni?”
28Suka amsa, “Mun ga a zahiri cewa Ubangiji yana tare da kai; saboda haka muka ce, ‘Dole rantsuwa ta kasance tsakaninmu da kai.’ Bari mu yi yarjejjeniya da kai 29cewa ba za ka cuce mu ba, kamar yadda ba mu fitine ka ba, amma muka yi maka kirki, muka kuma sallame ka cikin salama. Yanzu kuwa kai albarkatacce ne na Ubangiji.”
30Sai Ishaku ya shirya musu liyafa, suka ci suka kuma sha. 31Kashegari da sassafe sai mutanen suka yi wa juna rantsuwa. Sa’an nan Ishaku ya sallame su, suka kuwa tafi cikin salama.
32A wannan rana bayin Ishaku suka zo suka faɗa masa game da rijiyar da suka haƙa. Suka ce, “Mun sami ruwa!” 33Sai ya kira ta Shiba,#26.33 Shiba yana iya nufin rantsuwa ko kuma bakwai. don haka har wa yau ana kira garin Beyersheba.#26.33 Beyersheba yana iya nufin rijiyar rantsuwa ko kuwa rijiyar bakwai.
34Sa’ad da Yaƙub ya kai shekaru arba’in da haihuwa, sai ya auri Yudit ’yar Beyeri mutumin Hitti, da kuma Basemat ’yar Elon mutumin Hitti. 35Su ne suka zama sanadin baƙin ciki ga Ishaku da Rebeka.

Currently Selected:

Farawa 26: SRK

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in