11
Mutuwar Lazarus
1To, an yi wani mutum mai suna Lazarus wanda ya yi rashin lafiya. Shi daga Betani ne, ƙauyen su Maryamu da ’yar’uwarta Marta. 2Maryamun nan kuwa, wadda ɗan’uwanta Lazarus yake rashin lafiya, ita ce ta zuba wa Ubangiji turare ta kuma goge ƙafafunsa da gashin kanta. 3Saboda haka ’yan’uwansa mata suka aika da saƙo wa Yesu cewa, “Ubangiji, wannan da kake ƙauna yana rashin lafiya.”
4Sa’ad da ya ji haka, sai Yesu ya ce, “Wannan rashin lafiya ba zai kai ga mutuwa ba. A’a, sai dai don a ɗaukaka Allah a kuma ɗaukaka Ɗan Allah ta wurin wannan.” 5Yesu kuwa yana ƙaunar Marta da ’yar’uwarta da kuma Lazarus. 6Duk da haka sa’ad da ya ji Lazarus ba shi da lafiya, sai ya ƙara kwana biyu a inda yake.
7Sai ya ce wa almajiransa, “Mu koma Yahudiya.”
8Sai suka ce, “Rabbi, ba da daɗewa ba ne Yahudawa suka nemi su jajjefe ka, duk da haka za ka koma can?”
9Yesu ya amsa ya ce, “Ba sa’a goma sha biyu ce yini guda ba? Mutumin da yake tafiya da rana ba zai yi tuntuɓe ba gama yana ganin hasken duniyan nan. 10Sai a sa’ad da yake tafiya da dare ne zai yi tuntuɓe, don ba shi da haske.”
11Bayan ya faɗa haka, sai ya ƙara ce musu, “Abokinmu Lazarus ya yi barci, amma za ni in tashe shi.”
12Almajiransa suka ce, “Ubangiji, in barci ne yake, to, ai, zai sami sauƙi.” 13Yesu kuwa yana magana mutuwarsa ce, amma almajiransa suka ɗauka yana nufin barcin gaskiya ne.
14Saboda haka sai ya gaya musu a fili cewa, “Lazarus ya mutu, 15amma saboda ku na yi farin ciki da ba na can, domin ku gaskata. Amma mu dai je wurinsa.”
16Sai Toma (wanda ake kira Didaimus) ya ce wa sauran almajiran, “Mu ma mu je, mu mutu tare da shi.”
Yesu ya yi wa ’yan’uwan Lazarus mata ta’aziyya
17Da isowarsa, Yesu ya tarar Lazarus ya riga ya yi kwana huɗu a kabari. 18Betani bai kai mil biyu ba daga Urushalima, 19Yahudawa da yawa kuwa suka zo wurin Marta da Maryamu don su yi musu ta’aziyya, saboda rasuwar ɗan’uwansu. 20Sa’ad da Marta ta ji cewa Yesu yana zuwa, sai ta fita don ta tarye shi, amma Maryamu ta zauna a gida.
21Sai Marta ta ce wa Yesu, “Ubangiji, da kana nan da ɗan’uwana bai mutu ba. 22Amma na san cewa ko yanzu ma Allah zai ba ka duk abin da ka roƙa.”
23Yesu ya ce mata, “Ɗan’uwanki zai sāke tashi.”
24Marta ta amsa ta ce, “Na sani zai sāke tashi a tashin matattu a rana ta ƙarshe.”
25Yesu ya ce mata, “Ni ne tashin matattu da kuma rai. Duk wanda ya gaskata da ni zai rayu, ko ya mutu; 26kuma duk wanda yake raye ya kuma gaskata da ni ba zai taɓa mutuwa ba. Kin gaskata wannan?”
27Sai ta ce masa, “I, Ubangiji, na gaskata kai ne Kiristi, Ɗan Allah, mai zuwa cikin duniya.”
28Bayan ta faɗa haka kuwa, sai ta koma ta je ta kira ’yar’uwarta Maryamu a gefe. Ta ce, “Ga Malam ya zo, kuma yana kiranki.” 29Sa’ad da Maryamu ta ji haka sai ta yi wuf ta tafi wurinsa. 30Yesu dai bai riga ya shiga ƙauyen ba tukuna, har yanzu yana inda Marta ta tarye shi. 31Da Yahudawan da suke tare da Maryamu a cikin gida, suke mata ta’aziyya, suka ga ta yi wuf ta fita, sai suka bi ta, suna tsammani za tă kabarin ne tă yi kuka a can.
32Sa’ad da Maryamu ta kai inda Yesu yake, ta kuma gan shi, sai ta fāɗi a gabansa ta ce, “Ubangiji, da kana nan, da ɗan’uwana bai mutu ba.”
33Da Yesu ya ga tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita ma suna kuka, sai ya yi juyayi ƙwarai a ruhu ya kuma damu. 34Sai ya yi tambaya ya ce, “Ina kuka sa shi?”
Suka amsa suka ce, “Ubangiji zo ka gani.”
35Yesu ya yi kuka.
36Sai Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake ƙaunarsa!”
37Amma waɗansunsu suka ce, “Anya, wanda ya buɗe wa makahon nan idanu, ba zai iya yin wani abu yă hana wannan mutum mutuwa ba?”
Yesu ya tā da Lazarus daga matattu
38Yesu, har yanzu cike da juyayi, ya zo kabarin. Kogo ne da aka rufe bakin da dutse. 39Sai Yesu ya ce, “Ku kawar da dutsen.”
Marta, ’yar’uwan mamacin ta ce, “Ubangiji, yanzu, ai, zai yi wari, don yau kwanansa huɗu ke nan a can.”
40Sai Yesu ya ce, “Ban gaya miki cewa in kin gaskata za ki ga ɗaukakar Allah ba?”
41Saboda haka suka kawar da dutsen. Sa’an nan Yesu ya dubi sama ya ce, “Uba, na gode maka da ka saurare ni. 42Na san kullum kakan saurare ni, na dai faɗa haka ne saboda amfanin mutanen nan da suke tsaitsaye, don su gaskata cewa kai ka aiko ni.”
43Sa’ad da ya faɗa haka, sai Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce, “Lazarus, ka fito!” 44Sai mamacin ya fito, hannuwansa da ƙafafunsa a daure da ƙyallayen lilin, fuskarsa kuwa an naɗe da mayafi.
Yesu ya ce musu, “Ku tuɓe kayan bizo, ku bar shi yă tafi.”
An ƙulla shawara a kashe Yesu
(Mattiyu 26.1-5; Markus 14.1,2; Luka 22.1,2)
45Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo don su ziyarci Maryamu, suka kuma ga abin da Yesu ya yi, suka ba da gaskiya gare shi. 46Amma waɗansunsu suka je wurin Farisiyawa suka gaya musu abin da Yesu ya yi. 47Sai manyan firistoci da Farisiyawa suka kira taron Majalisa.
Suka yi tambaya suna cewa, “Me muke yi ne? Ga mutumin nan yana yin abubuwan banmamaki masu yawa. 48In fa muka ƙyale shi ya ci gaba da haka, kowa zai gaskata da shi, Romawa kuma su zo su karɓe wurinmu su kuma ƙwace ƙasarmu.”
49Sai waninsu, mai suna Kayifas, wanda ya kasance babban firist a shekarar ya ce, “Ku dai ba ku san kome ba! 50Ba ku gane ba, ai, gwamma mutum ɗaya yă mutu saboda mutane da duk ƙasar ta hallaka.”
51Bai faɗa haka bisa nufinsa ba, sai dai a matsayinsa na babban firist a shekarar, ya yi annabci ne cewa Yesu zai mutu saboda ƙasar Yahudawa, 52ba don ƙasan nan kaɗai ba amma don yă tattaro ’ya’yan Allah da suke warwatse ma, su zama ɗaya. 53Saboda haka, daga wannan rana suka ƙulla su ɗauke ransa.
54Saboda haka Yesu bai ƙara tafiya a cikin Yahudawa a sarari ba. A maimako haka sai ya janye zuwa yankin kusa da hamada, a wani ƙauye da ake kira Efraim, inda ya zauna da almajiransa.
55Sa’ad da lokaci ya yi kusa a yi Bikin Ƙetarewa na Yahudawa, da yawa suka haura daga ƙauyuka zuwa Urushalima, don su tsarkake kansu kafin Bikin Ƙetarewa. 56Suka yi ta neman Yesu, da suke a tsaitsaye a filin haikali kuwa suka dinga tambayar juna, suna cewa, “Me kuka gani? Anya, zai zo Bikin kuwa?” 57Manyan firistoci da Farisiyawa tuni sun riga sun yi umarni cewa duk wanda ya san inda Yesu yake, yă faɗa don su kama shi.