YouVersion Logo
Search Icon

Yohanna Gabatarwa

Gabatarwa
Gabatarwa
Yohanna, Bishara ta huɗu, ta mai da hankali a kan matsayin Yesu kamar Kiristi da kuma kamar madawwamin Kalman Allah wanda yake tare da Allah tun farkon halitta. Wannan ya bambanta Yohanna daga bisharu uku na farko. Mattiyu, Markus, da Luka; waɗanda suka mai da hankali a ba da tarihin don nuna cewa Yesu shi ne cikar alkawarin Allah ga Isra’ila. Saboda wannan dalili, masana da yawa sun ba da gaskiya cewa an rubuta Yohanna don a amsa wa waɗanda suka yi shakka cewa Yesu shi ne Kiristi. Yohanna ya bayyana mu’ujizai bakwai (alamu) na Yesu ya kuma yi amfani da waɗannan mu’ujizai don yă nuna koyarwar Yesu yă kuma nuna shi a matsayin Ɗan Allah. Ta wurin yin amfani da misalai don yă nuna Yesu kamar ruwa, haske, ƙofa, da kuma burodi, Yohanna ya yi ƙoƙari yă bi da masu karatu zuwa cikin mulkin Allahn da Yesu ya shirya dominsu.

Currently Selected:

Yohanna Gabatarwa: SRK

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in