YouVersion Logo
Search Icon

Far 27

27
Yakubu Ya Karɓi Albarka daga wurin Ishaku
1Lokacin da Ishaku ya tsufa, idanunsa kuma suka yi duhu har ba ya iya gani, sai ya kira Isuwa babban ɗansa, ya ce masa, “Ɗana!”
Sai ya amsa, “Ga ni nan.”
2Ishaku ya ce, “Ga shi, na tsufa, ban san ranar rasuwata ba. 3Yanzu fa, ka ɗauki makamanka, da kwarinka da bakanka, ka tafi jeji ka farauto mini nama, 4ka shirya mini abinci mai daɗi irin wanda nake so, ka kawo mini in ci, don in sa maka albarka kafin in rasu.”
5Rifkatu kuwa tana ji lokacin da Ishaku yake magana da ɗansa Isuwa. Don haka, sa'ad da Isuwa ya tafi jeji garin ya farauto nama ya kawo, 6sai Rifkatu ta ce wa ɗanta Yakubu, “Na ji mahaifinka ya yi magana da ɗan'uwanka Isuwa, ya ce, 7‘Kawo mini nama, ka shirya mini abinci mai daɗi in ci, in sa maka albarka a gaban Ubangiji kafin in rasu.’ 8Yanzu fa, ɗana, ka biye wa maganata yadda zan umarce ka. 9Je ka garke, ka kamo 'yan awaki biyu kyawawa, domin in shirya abinci mai daɗi da su domin mahaifinka, irin wanda yake so. 10Kai kuwa ka kai wa mahaifinka, ya ci, domin ya sa maka albarka kafin ya rasu.”
11Amma Yakubu ya ce wa Rifkatu mahaifiyarsa, “Ga shi fa, ɗan'uwana Isuwa gargasa ne, ni kuwa mai sulɓi ne. 12Watakila, baba zai lallaluba ni, zai kuwa ce, ruɗinsa nake yi, in kuwa jawo wa kaina la'ana maimakon albarka.”
13Sai mahaifiyarsa ta ce masa, “La'anarka ta faɗo bisa kaina, ɗana. Kai dai ka yi biyayya da maganata. Je ka, ka kamo mini.” 14Ya tafi ya kamo su, ya kawo su ga mahaifiyarsa, mahaifiyarsa kuwa ta shirya abinci mai daɗi irin wanda mahaifinsa yake so. 15Rifkatu ta ɗauki riguna mafi kyau na babban ɗanta Isuwa waɗanda suke wurinta cikin gida, ta kuwa sa wa Yakubu ƙaramin ɗanta su, 16fatun 'yan awakin kuwa ta naɗe wa hannuwansa, da sashen dokin wuyansa mai sulɓi. 17Sai ta bai wa ɗanta, Yakubu, abinci mai daɗin ci da gurasar da ta shirya.
18Ya kuwa shiga wurin mahaifinsa, ya ce, “Baba.”
Mahaifin ya ce, “Ga ni, wane ne kai, ya ɗana?”
19Yakubu ya ce wa mahaifinsa, “Ni ne Isuwa ɗan farinka. Na yi yadda ka faɗa mini, in ka yarda ka tashi ka ci naman da na harbo, domin ka sa mini albarka.”
20Amma Ishaku ya ce wa ɗansa, “Ƙaƙa aka yi ka same shi da sauri haka, ɗana?”
Sai ya amsa, “Domin Ubangiji, Allahnka, ya ba ni sa'a.”
21Ishaku kuwa ya ce wa Yakubu, “Matso kusa in ka yarda, don in lallaluba ka, ɗana, domin in hakikance ko kai ne ɗana Isuwa, ko babu.” 22Saboda haka Yakubu ya matsa kusa da Ishaku mahaifinsa, sai ya lallaluba shi, ya ce, “Murya, muryar Yakubu ce, amma hannuwa, hannuwan Isuwa ne.” 23Amma bai gane shi ba, gama hannuwansa gargasa ne kamar hannuwan ɗan'uwansa Isuwa, saboda haka ya sa masa albarka. 24Ya ce, “Hakika, kai ne ɗana Isuwa?”
Ya amsa, “Ni ne.”
25Ya ce, “Kawo mini naman da ka harbo, in ci in sa maka albarka.” Sai ya kawo masa, ya kuwa ci, ya kawo masa ruwan inabi, ya sha. 26Mahaifinsa Ishaku kuwa ya ce masa, “Zo kusa ka sumbace ni, ɗana.” 27#Ibr 11.20 Don haka ya zo kusa ya sumbace shi. Ishaku ya sansana rigunansa, ya sa masa albarka, ya ce,
“Duba, ƙanshin ɗana
Yana kama da ƙanshin jeji
Wanda Ubangiji ya sa wa albarka!
28Allah ya ba ka daga cikin raɓar
sama,
Daga cikin ni'imar ƙasa,
Da hatsi a yalwace da ruwan inabi.
29 # Far 12.3 Bari jama'a su bauta maka,
Al'ummai kuma su sunkuya maka.
Za ka yi shugabancin 'yan'uwanka,
Allah ya sa 'ya'yan mahaifiyarka su
sunkuya maka.
La'ananne ne dukan wanda ya
la'anta ka,
Albarkatacce ne dukan wanda ya sa
maka albarka.”
30Ishaku yana gama sa wa Yakubu albarka, Yakubu yana fita daga gaban mahaifinsa ke nan sai ga Isuwa ɗan'uwansa ya komo daga farauta. 31Shi kuma ya shirya abinci mai daɗin ci, ya kawo wa mahaifinsa. Sai ya ce wa mahaifinsa, “In ka yarda baba, ka tashi, ka ci naman da na harbo don ka sa mini albarka.”
32Mahaifinsa Ishaku ya ce masa, “Wane ne kai?”
Ya amsa, “Ni ne ɗanka, ɗan farinka, Isuwa.”
33Ishaku kuwa ya yi makyarkyata ƙwarai, ya ce, “Wane ne wannan fa, da ya farauto naman ya kawo mini, na kuwa cinye kafin ka zo, har na sa masa albarka? – I, albarkatacce zai zama.”
34Da Isuwa ya ji kalmomin mahaifinsa, sai ya yi kūwwa da kuka mai tsananin gaske, ya ce wa mahaifinsa, “Ka sa mini albarka, har da ni ma, ya babana.”
35Amma ya ce, “Ɗan'uwanka ya zo cikin makirci, ya karɓe albarkarka.”
36 # Far 25.29-34 Isuwa ya ce, “Ba saboda haka ne aka raɗa masa suna Yakubu ba? Gama sau biyu ke nan yake yi mini ƙwace. Ya ƙwace mini matsayina na ɗan fari, ga shi kuma, yanzu ya ƙwace mini albarkata.” Sa'an nan ya ce, “Ba sauran albarkar da ka rage mini?”
37Ishaku ya amsa wa Isuwa ya ce, “Ga shi, na shugabantar da shi a kanka da dukan 'yan'uwansa na ba shi su, su zama barorinsa, na ba shi hatsi da ruwan inabi. Me zan yi maka kuma, ya ɗana?”
38 # Ibr 12.17 Sai Isuwa ya ce wa mahaifinsa, “Iyakar albarkar da kake da ita ke nan, baba? Har da ni ma ka sa mini albarka, babana.” Isuwa ya ta da murya ya yi kuka.
39 # Ibr 11.20 Sai Ishaku mahaifinsa ya amsa masa ya ce,
“Ga shi, ni'imar ƙasar za ta nisanci
mazauninka,
Raɓar samaniya can ƙwanƙoli za
ta nisance ka.
40 # Far 36.8; 2Sar 8.20 Ta wurin takobinka za ka rayu
Za ka yi wa ɗan'uwanka barantaka,
Amma sa'ad da ka ɓalle,
Za ka kakkarye karkiyarsa daga
wuyanka.”
41Isuwa dai ya ƙi jinin Yakubu saboda albarkar da mahaifinsa ya sa masa. Sai Isuwa ya ce a ransa, “Kwanakin makoki domin mahaifina suna gabatowa, sa'an nan zan kashe Yakubu ɗan'uwana.”
42Amma maganganun Isuwa babban ɗanta suka kai a kunnen Rifkatu. Saboda haka, sai ta aika aka kirawo Yakubu ƙaramin ɗanta. Ta ce masa, “Ga shi, ɗan'uwanka Isuwa, yana ta'azantar da kansa da nufin ya kashe ka, ya ɗau fansa. 43Domin haka, ɗana, ka ji muryata, ka tashi ka gudu zuwa wurin Laban ɗan'uwana a Haran, 44ka zauna tare da shi 'yan kwanaki, har zafin fushin ɗan'uwanka ya huce, 45ya manta da abin da ka yi masa, sa'an nan zan aika in komo da kai daga can. Don me zan rasa ku, ku biyu a rana ɗaya?”
Ishaku Ya Aika da Yakubu wurin Laban
46Rifkatu kuwa ta ce wa Ishaku, “Na gaji da raina saboda matan Hittiyawa. Idan Yakubu zai auri ɗaya daga cikin waɗannan mata na Hittiyawa, wato daga matan ƙasar, wane amfani raina zai daɗa mini?”

Currently Selected:

Far 27: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in