YouVersion Logo
Search Icon

Far 47

47
1Yusufu ya shiga ya yi magana da Fir'auna, ya ce, “Mahaifina da 'yan'uwana, da garkunansu na awaki da na tumaki, da garkunan shanu, da dukan abin da suka mallaka, sun zo daga ƙasar Kan'ana, yanzu suna ƙasar Goshen.” 2Daga cikin 'yan'uwansa kuma ya ɗauki mutum biyar ya gabatar da su a gaban Fir'auna.
3Sai Fir'auna ya ce wa 'yan'uwan nan nasa, “Mece ce sana'arku?”
Suka amsa wa Fir'auna, suka ce, “Ranka ya daɗe, mu makiyaya ne, kamar yadda iyayenmu suke.” 4Suka kuma ce wa Fir'auna, “Ranka ya daɗe, mun zo baƙunci ne cikin ƙasar, gama ba wurin kiwo domin garkunan bayinka, gama yunwa ta tsananta a ƙasar Kan'ana. Yanzu muna roƙonka, ka yarda wa bayinka su zauna a ƙasar Goshen.”
5Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Mahaifinka da 'yan'uwanka sun zo wurinka. 6Ƙasar Masar tana gabanka. Ka zaunar da mahaifinka da 'yan'uwanka a ƙasa mai kyau, bari su zauna a ƙasar Goshen. In kuma ka san da waɗansu waɗanda suka dace a cikinsu, ka sa su su lura da shanuna.”
7Yusufu kuwa ya shigo da Yakubu mahaifinsa, ya tsai da shi a gaban Fir'auna, Yakubu kuwa ya sa wa Fir'auna albarka. 8Fir'auna kuma ya ce wa Yakubu, “Nawa ne shekarun haihuwarka?”
9Yakubu ya ce wa Fir'auna, “Shekaruna na zaman baƙuncina, shekara ce ɗari da talatin, shekaruna kima ne cike kuma da wahala, ba su kuwa kai yawan shekarun kakannina ba, cikin baƙuncinsu.” 10Yakubu kuwa ya sa wa Fir'auna albarka, sa'an nan ya fita daga gaban Fir'auna. 11Sai Yusufu ya zaunar da mahaifinsa da 'yan'uwansa, ya kuwa ba su mahalli a ƙasar Masar, cikin ƙasa mafi kyau a ƙasar Remesse, kamar yadda Fir'auna ya umarta. 12Yusufu ya bai wa mahaifinsa da 'yan'uwansa da dukan iyalin gidan mahaifinsa abinci, bisa ga yawan 'ya'yansu.
Hidimar Yusufu a Lokacin Yunwa
13A yanzu cikin ƙasar duka, ba abinci, gama yunwar ta tsananta ƙwarai, har ƙasar Masar da ƙasar Kan'ana suka matsu saboda yunwar. 14Yusufu kuwa ya ƙwalƙwale dukan kuɗin da yake akwai a ƙasar Masar da a ƙasar Kan'ana, domin hatsin da suka saya. Yusufu kuma ya kawo kuɗin cikin gidan Fir'auna. 15Sa'ad da aka kashe kuɗin da yake a Masar duka da na ƙasar Kan'ana, Masarawa duka suka zo wurin Yusufu, suka ce, “Ka ba mu abinci, don me za mu mutu a kan idonka? Gama kuɗinmu sun ƙare.”
16Yusufu ya amsa, ya ce, “Ku ba da shanunku, ni kuwa zan ba ku abinci a madadin shanunku in kuɗinku sun ƙare.” 17Saboda haka suka kai wa Yusufu dabbobinsu, sai Yusufu ya ba su abinci madadin dawakai da garkunan awaki da na tumaki, da garkunan shanu da na jakai, ya tallafe su da abinci a madadin dabbobinsu duka a wannan shekara.
18Sa'ad da wannan shekara ta ƙare, sai suka zo wurinsa a shekara ta biyu, suka ce masa, “Ranka ya daɗe. Ba za mu ɓoye wa shugabanmu ba cewa kuɗinmu duka mun kashe, garkunan dabbobin kuma sun zama naka. Banda jikunanmu da gonakunmu, ba kuwa abin da ya rage mana. 19Kada ka bar mu mu mutu, ka yi wata dabara! Kada ka bari mu rasa gonakinmu. Ka musaye mu da abinci, mu da gonakunmu. Mu kuwa za mu zama bayin Fir'auna, ka kuma ba mu iri domin mu rayu, kada mu mutu don kuma kada ƙasar ta zama kango.”
20Ta haka Yusufu ya saya wa Fir'auna ƙasar Masar duka, gama Masarawa duka sun sayar da saurukansu, saboda yunwa ta tsananta musu. Ƙasar ta zama halaliyar Fir'auna. 21Yusufu ya mai da jama'ar bayi daga wannan kan iyaka na Masar zuwa wancan. 22Sai gonakin firistoci ne kaɗai bai saya ba, gama firistocin suna da rabo wanda Fir'auna ya yanka musu, da rabon da Fir'auna yake ba su suke zaman gari, sabili da haka ba su sayar da gonakinsu ba. 23Yusufu ya ce wa jama'ar, “Ga shi, a yau na saya wa Fir'auna ku da gonakinku. Yanzu fa, ga iri dominku, za ku shuka gonakin. 24Da haka za ku ba da kashi ɗaya cikin biyar ga Fir'auna, kashi huɗu cikin biyar kuwa ya zama naku din iri na shuka a gonakinku, don kuma abincinku, da na iyalan gidanku, da na 'yan ƙanananku.”
25Suka ce, “Ka ceci rayukanmu, in ko ya gamshe ka, ya shugaba, mā zama bayin Fir'auna.” 26Sai Yusufu ya kafa doka daga wannan rana har wa yau game da ƙasar Masar wadda ta ce, Fir'auna zai sami kashi ɗaya daga cikin biyar, sai dai gonakin firistoci kaɗai ne ba su zama na Fir'auna ba.
Wasiyyar Yakubu
27Ta haka fa Isra'ila ya yi zamansa a ƙasar Masar a ƙasar Goshen, suka kuwa sami mahalli a cikinta suka hayayyafa suka riɓaɓɓanya ƙwarai. 28Yakubu kuma ya zauna a ƙasar Masar shekara goma sha bakwai, don haka kwanakin Yakubu, wato shekarun ransa, shekara ce ɗari da arba'in da bakwai. 29#Far 49.29-32; 50.6 A sa'ad da lokaci ya gabato da Isra'ila zai mutu, ya kira ɗansa Yusufu ya ce masa, “Idan zan sami tagomashi a idonka, ka sa hannunka a ƙarƙashin cinyata, ka ɗau alkawari za ka aikata mini aminci da gaskiya. Kada ka binne ni a Masar, 30amma bari in kwanta tare da kakannina, ka ɗauke ni daga Masar, ka binne ni a makabartarsu.”
Ya amsa ya ce, “Zan aikata yadda ka faɗa.”
31Sai Yakubu ya ce, “Rantse mini.” Sai Yusufu ya rantse masa. Sa'an nan sai Isra'ila ya mai da kai bisa kan gadonsa.

Currently Selected:

Far 47: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in