Luk 12
12
Faɗaka a kan Makirci
1 #
Mat 16.6; Mar 8.15 Sa'an nan kuwa da dubban mutane suka taru har suna tattaka juna, da farko ya yi magana da almajiransa. Ya fara cewa, “Ku yi hankali da yistin Farisiyawa, wato, makirci. 2#Mar 4.22; Luk 8.17 Ba abin da yake rufe da ba zai tonu ba, ko kuwa abin da yake ɓoye da ba za a bayyana ba. 3Don haka, kome kuka faɗa a asirce, za a ji shi a sarari. Abin kuma da kuka yi raɗa a loloki, za a yi shelarsa daga kan soraye
Wanda za a Ji Tsoro
(Mat 10.28-31)
4“Ya ku masoyana, ina dai gaya muku, kada ku ji tsoron masu kisan mutum, bayan sun kashe kuwa, ba abin da za su iya yi. 5Amma zan gaya muku wanda za ku tsorata. Ku ji tsoron wannan da in ya kashe, yana da ikon jefawa a cikin Gidan Wuta. Hakika, ina gaya muku, shi za ku ji tsoro! 6Ashe, ba gwara biyar ne kobo biyu ba? Ko ɗayarsu kuwa Allah bai manta da ita ba. 7Kai! ko da gashin kanku ma duk a ƙidaye yake. Kada ku ji tsoro. Ai, martabarku ta fi ta gwara masu yawa.”
Bayyana Yarda da Almasihu a gaban Mutane
(Mat 10.32-33; 12.32)
8“Ina kuma gaya muku, kowa ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, Ɗan Mutum ma zai bayyana yarda a gare shi a gaban mala'ikun Allah. 9Wanda kuwa ya yi musun sanina a gaban mutane, za a yi musun saninsa a gaban mala'ikun Allah. 10#Mat 12.32; Mar 3.29 Kowa ya kushe wa Ɗan Mutum, ā gafarta masa, amma wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba. 11#Mat 10.19,20; Mar 13.11; Luk 21.14,15 Sa'ad da suka kai ku gaban majami'u, da mahukunta da shugabanni, kada ku damu da yadda za ku mai da jawabi, ko kuwa abin da za ku faɗa, 12domin Ruhu Mai Tsarki zai koya muku abin da ya kamata ku faɗa a lokacin.”
Misali na Mai Arziki Marar Azanci
13Sai wani a cikin taron ya ce masa, “Malam, kă ce wa ɗan'uwana ya raba gādo da ni.” 14Amma Yesu ya ce masa, “Haba kai kuwa, wa ya sa ni in zama muku alƙali, ko in raba muku gādo?” 15Ya kuma ce musu, “Ku kula fa, ku yi nesa da kowane irin kwaɗayi, don yawan kaya ba shi ne rai ba.” 16Sai ya ba su misali ya ce, “Gonar wani mai arziki ta yi albarka ƙwarai. 17Sai ya ce a ransa, ‘To, ƙaƙa zan yi? Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonata.’ 18Ya kuma ce, ‘To, ga abin da zan yi. Sai in rushe rumbunana, in gina waɗansu manya, in zuba duk amfanin gonata da kayana a ciki. 19Zan kuma ce wa raina, “Lalle ina da kaya masu yawa a jibge, tanadin shekara da shekaru. Bari in huta, in yi ta ci, in yi ta sha, ina shagali.” ’ 20Amma Allah ya ce masa, ‘Kai marar azanci! A daren nan za a karɓi ranka. To, kayan da ka tanada, na wa za su zama?’ 21Haka, wanda ya tanada wa kansa dukiya yake, ba shi kuwa da wani tanadi a gun Allah.”
Damuwa da Alhini
(Mat 6.25-34)
22Sai ya ce wa almajiransa, “Don haka, ina gaya muku, kada ku damu da batun rayuwarku game da abin da za ku ci, ko kuma jikinku, abin da za ku yi sutura. 23Domin rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi tufafi. 24Ku dubi dai hankaki! Ai, ba sa shuka, ba sa girbi, ba su da taska ko rumbu, amma kuwa Allah yana cishe su. Sau nawa martabarku ta ninka ta tsuntsaye!” 25Wane ne a cikinku don damuwarsa zai iya ƙara ko da taƙi ga tsawon rayuwarsa? 26To, in ba za ku iya yin ƙaramin abu irin wannan ba, don me kuke damuwa da sauran? 27#1Sar 10.4-7; 2Tar 9.3-6 Ku dubi dai furanni yadda suke girma, ba sa aikin fari, ba sa na baƙi, duk da haka, ina gaya muku, ko Sulemanu ma, shi da adonsa duk, bai taɓa yin adon da ya fi na ɗayansu ba. 28To, ga shi Allah yana ƙawata tsire-tsiren jeji ma haka, waɗanda yau suke a raye, gobe kuwa a jefa su a murhu, balle ku? Ya ku masu ƙarancin bangaskiya! 29Ku ma kada ku damu a kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kada kuwa ku yi alhini. 30Ai, al'umman duniya suna ta neman duk irin waɗannan abubuwa, ku kuwa, Ubanku ya san kuna bukatarsu. 31Ku ƙwallafa rai ga al'amuran Mulkin Allah, sai a ƙara muku da waɗannan abubuwa kuma.
Tara Dukiya a Sama
(Mat 6.19-21)
32“Ya ku ɗan ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, domin Ubanku na jin daɗin ba ku rabo a cikin Mulkin. 33Ku sayar da mallakarku, ku bayar taimako. Ku samar wa kanku jakar kuɗi da ba ta tsufa, wato, dukiya marar yankewa ke nan a Sama, inda ba ɓarawon da zai gabato, ba kuma asun da zai ɓāta, 34don kuwa inda dukiyarka take, a nan zuciyarka ma take.”
Bayin da suke a Faɗake
35 #
Mat 25.1-13
“Ku yi ɗamara, fitilunku na kunne. 36#Mar 13.34-36Ku dai zama kamar mutane masu jiran ubangijinsu ya dawo daga gidan biki, da zarar ya ƙwanƙwasa su buɗe masa. 37Albarka tā tabbata ga bayin nan waɗanda ubangijinsu da zuwansa zai same su a faɗake. Hakika, ina gaya muku, zai yi ɗamara, ya ce su zauna cin abinci, sa'an nan ya bi ta kan kowannensu yana yi masa hidima. 38In kuwa ya zo da tsakar dare ne, ko kuwa bayan tsakar dare, ya same su a faɗake, bayin nan masu albarka ne. 39#Mat 24.43,44 Amma dai ku sani, da maigida zai san lokacin da ɓarawo zai zo, da ya zauna a faɗake, ya hana a shiga masa gida. 40Ku ma sai ku zauna a kan shiri, domin a lokacin da ba ku zata ba Ɗan Mutum zai zo.”
Amintaccen Bawa ko Marar Aminci
(Mat 24.45-51)
41Sai Bitrus ya ce, “Ya Ubangiji, mu ne kake faɗa wa wannan misali, ko kuwa na kowa da kowa ne?” 42Ubangiji ya ce, “Wane ne amintaccen wakilin nan mai hikima, da ubangidansa zai ba shi riƙon gidansa, yă riƙa ba su abincinsu a kan kari? 43Albarka tā tabbata ga bawan da, in ubangidansa ya dawo, zai samu yana yin haka. 44Hakika, ina gaya muku, sai ya ɗora shi a kan dukan mallaka tasa. 45In kuwa bawan nan ya ce a ransa, ‘Ubangijina ya jinkirta zuwansa,’ sa'an nan ya soma dūkan barori, maza da mata, ya shiga ci da sha har yana buguwa, 46ai, ubangijin wannan bawa zai zo a ranar da bai zata ba, a lokacin kuma da bai sani ba, yă farfasa masa jiki da bulala, ya ba shi rabonsa tare da marasa riƙon amana. 47Bawan nan kuma wanda ya san nufin ubangijinsa, bai yi shiri ba, bai kuma bi nufinsa ba, za a yi masa matsanancin dūka, 48Wanda kuwa bai san nufin ubangijinsa ba, ya kuma yi abin da ya isa dūka, za a doke shi kaɗan. Duk wanda aka ba abu mai yawa, a gunsa za a tsammaci abu mai yawa. Wanda kuma aka danƙa wa abu mai yawa, abu mafi yawa za a nema a gare shi.”
Yesu Ya Kawo Rabuwa
(Mat 10.34-36)
49“Wuta ce na zo in zuba wa duniya. Sona fa? A ce ta huru! 50#Mar 10.38 Ina da baftismar da za a yi mini, na kuwa ɗokanta ƙwarai har a yi mini ita! 51Kuna tsammani na zo ne in kawo salama a duniya? A'a, ina gaya muku, sai dai rabuwa. 52Nan gaba, a gida guda mutum biyar za su kasu biyu, uku na gāba da biyu, biyu kuma na gāba da uku. 53#Mika 7.6 Ta haka, za su rabu. Uba yana gāba da ɗansa, ɗan kuma yana gāba da ubansa, uwa tana gāba da 'ya tata, 'yar kuma tana gāba da uwa tata, suruka tana gāba da matar ɗanta, matar ɗan kuma tana gāba da suruka tata.”
Gane Yanayin Lokatai
(Mat 16.1-4; Mar 8.11-13)
54Ya kuma ce wa taron, “In kun ga girgije yana tasowa daga yamma, nan da nan kukan ce, ‘Za a yi ruwa.’ Sai kuwa a yi. 55In kuwa kun ga iskar kudu tana busowa, kukan ce, ‘Za a yi matsanancin zafi.’ Sai kuwa a yi. 56Munafukai! Kuna iya gane yanayin ƙasa da na sararin sama, amma me ya sa ba ku iya gane alamun zamanin ba?”
Yi Jiyayya da Mai Ƙararka
(Mat 5.25-26)
57“Me ya sa ku da kanku ma ba kwa iya rarrabewa da abin da yake daidai? 58Misali, in kuna tafiya zuwa gaban shari'a da mai ƙararku, sai ku yi ƙoƙari ku yi jiyayya da shi tun a hanya, don kada ya ja ku zuwa gaban alƙali, alƙali kuma ya miƙa wa ɗan doka, ɗan doka kuma ya jefa ku a kurkuku. 59Ina gaya muku, lalle ba za ku fita ba, sai kun biya duka, ba sauran ko anini.”
Currently Selected:
Luk 12: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

: