Luk 15
15
Misali na Ɓatacciyar Tunkiya
(Mat 18.12-14)
1 #
Luk 5.29,30 To, sai duk masu karɓar haraji da masu zunubi suka yi ta matsowa wurinsa su saurare shi. 2Sai Farisiyawa da malaman Attaura suka riƙa gunaguni suna cewa, “Haba! Wannan mutum yana karɓar masu zunubi, har ma tare suke cin abinci!”
3Sai ya ba su wannan misali ya ce. 4“In waninku yana da tumaki ɗari, ɗayarsu ta ɓace, to, ba sai ya bar tasa'in da taran nan a makiyaya, ya bi sawun wadda ta ɓata, har ya same ta ba? 5In kuwa ya same ta, sai ya saɓo ta a kafaɗa, yana farin ciki. 6In ya dawo gida, sai ya tara abokansa da maƙwabta ya ce musu, ‘Ku taya ni farin ciki, don na samo tunkiyata da ta ɓata.’ 7Ina dai gaya muku, haka kuma, za a yi farin ciki a Sama, a kan mai zunubi guda da ya tuba, fiye da kan adalai tasa'in da tara waɗanda ba su bukatar tuba.”
Misali na Ɓataccen Kuɗi
8“Ko kuwa wace mace ce, in tana da kuɗi azurfa guda goma, in ta yar da ɗaya, ba sai ta kunna fitila ta share gidan, ta yi ta nacin nemansa, har ta same shi ba? 9In kuwa ta same shi, sai ta tara ƙawayenta da maƙwabta mata, ta ce musu, ‘Ku taya ni farin ciki, don na sami kuɗin nan da na yar.’ 10Haka nake gaya muku, abin farin ciki ne ga mala'ikun Allah in mai zunubi guda ya tuba.”
Misali na Ɓataccen Ɗa
11Ya kuma ce, “An yi wani mutum mai 'ya'ya biyu maza. 12Sai ƙaramin ya ce wa ubansa, ‘Baba, ba ni rabona na gādo.’ Sai uban ya raba musu dukiyarsa. 13Bayan 'yan kwanaki kaɗan sai ƙaramin ya tattara duk mallakarsa, ya kama hanya zuwa ƙasa mai nisa. A can ya fallasar da kayansa a wajen masha'a. 14Da ya ɓad da kome kakat, aka yi babbar yunwa a ƙasar, sai ya shiga fatara. 15Ya je ya rāɓu da wani ɗan ƙasar, shi kuwa ya tura shi makiyayar kiwon alade. 16Har ma ya so ya cika cikinsa da kwasfar da aladu suke ci, amma ba wanda ya ba shi wani abu 17Amma da ya tara hankalinsa sai ya ce, ‘Kaitona! Nawa ne daga cikin barorin ubana da suke da abinci, da yake kamar ƙasa a gare su! Ga ni a nan kuwa, yunwa tana kisana! 18Zan tashi, in tafi gun ubana, in ce masa, “Baba, na yi wa Mai Sama zunubi, na kuma saɓa maka. 19Ban ma cancanci a ƙara kirana ɗanka ba. Ka mai da ni kamar ɗaya daga cikin barorinka.” ’ 20Sai ya tashi, ya taho wurin ubansa. Amma tun yana daga nesa, sai ubansa ya hango shi, tausayi ya kama shi, ya yiwo gudu, ya rungume shi, ya yi ta sumbatarsa. 21Sai kuma ɗan ya ce masa, ‘Baba, na yi wa Mai Sama zunubi, na kuma saɓa maka. Ban ma cancanci a ƙara kirana ɗanka ba.’ 22Amma uban ya ce wa bayinsa, ‘Maza ku kawo riga mafi kyau, ku sa masa. Ku sa masa zobe da takalma, 23a kuma kawo kiwataccen ɗan maraƙin nan, a yanka, mu ci, mu yi murna. 24Don ɗan nan nawa dā ya mutu ne, amma a yanzu ya komo, dā ya ɓata, amma a yanzu an same shi.’ Sai suka yi ta farin ciki.
25“A sa'an nan kuwa, babban ɗansa yana gona. Yana dawowa, ya yi kusa da gida ke nan, sai ya ji ana kaɗe-kaɗe da raye-raye. 26Sai ya kira wani baran gidan, ya tambayi dalilin wannan abu. 27Shi kuwa ya ce masa, ‘Ai, ɗan'uwanka ne ya dawo, tsohonku ya yanka kiwataccen ɗan maraƙin nan saboda ya sadu da shi lafiya ƙalau.’ 28Amma wan ya yi fushi, ya ƙi shiga. Ubansa kuwa ya fito, ya yi ta rarrashinsa. 29Amma ya amsa wa ubansa ya ce, ‘Dubi yawan shekarun nan da na bauta maka. Ban taɓa ta da umarninka ba. Duk da haka, ba ka taɓa ba ni ko ɗan taure ba, da za mu yi shagali tare da abokaina. 30Amma da ɗan nan naka ya zo, wanda ya fallasar da dukiyarka a kan karuwai, ga shi, ka yanka masa kiwataccen ɗan maraƙin nan!’ 31Sai uban ya ce masa, ‘Ya ɗana, ai, kullum kana tare da ni, duk abin da yake nawa naka ne. 32Ai kuwa, daidai ne a yi ta murna da farin ciki, don ɗan'uwan nan naka dā ya mutu, a yanzu ya komo, dā ya ɓata, amma an same shi.’ ”
Currently Selected:
Luk 15: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

: