Luk 23
23
Yesu a gaban Bilatus
(Mat 27.1-2,11-14; Mar 15.1-5; Yah 18.28-38)
1Duk taronsu sai suka tashi, suka kai shi gaban Bilatus. 2Sai suka fara kai ƙararsa, suna cewa, “Mun sami mutumin nan yana ɓad da jama'armu, yana hana a biya Kaisar haraji, yana cewa, shi ne Almasihu, sarki kuma.” 3Sai Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Ashe, kai ɗin nan, kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa ya ce, “Yadda ka faɗa.” 4Bilatus ya ce wa manyan firistoci da taro masu yawa, “Ban sami mutumin nan da wani laifi ba.” 5Sai suka fara matsa masa lamba, suna cewa, “Yana ta da hankalin jama'a, yana koyarwa a dukan ƙasar Yahudiya, tun daga ƙasar Galili har zuwa nan.”
Yesu a gaban Hirudus
6Da Bilatus ya ji haka, ya tambaya ko mutumin nan Bagalile ne. 7Da ya ji Yesu a ƙarƙashin mulkin Hirudus yake, sai ya aika da shi wurin Hirudus, don shi ma yana Urushalima a lokacin. 8Da Hirudus ya ga Yesu, ya yi murna ƙwarai, saboda tun da daɗewa yake son ganinsa, don ya riga ya ji labarinsa, yana kuma fata ya ga wata mu'ujiza da Yesu zai yi. 9Sai ya yi ta masa tambayoyi da yawa, amma bai amsa masa da kome ba. 10Manyan firistoci da malaman Attaura na nan a tsaitsaye, suna tsananta kai ƙararrakinsa ainun. 11Sai Hirudus da sojansa suka wulakanta shi, suka yi masa ba'a, da suka sa masa tufafi masu ƙawa kuma, suka mai da shi wurin Bilatus. 12A ran nan sai Hirudus da Bilatus suka yi sulhu, don dā abokan gāba ne.
An Hukunta wa Yesu Mutuwa
(Mat 27.15-26; Mar 15.6-15; Yah 18.39—19.16)
13Bilatus ya tara manyan firistoci da shugabanni da kuma jama'a, 14ya ce masu, “Kun kawo mini mutumin nan a kan, wai yana ɓad da jama'a, na kuwa tuhunce shi a gabanku, amma ban same shi da wani laifi a ƙararrakinsa da kuka kawo ba. 15Hirudus ma bai samu ba, don ya komo mana da shi. Ga shi kuwa, bai yi wani abu da ya cancanci kisa ba. 16Saboda haka, zan yi masa bulala in sake shi.” 17[A lokacin idi kuwa lalle ne ya sakar musu ɗaurarre guda.]
18Amma duk suka ɗauki ihu gaba ɗaya, suna cewa, “A yi da wannan ɗin, a sakar mana Barabbas!” 19(Barabbas shi ne wani mutum da aka jefa a kurkuku, saboda wani tawayen da aka yi a birni, da kuma kisankai.) 20Sai Bilatus ya sāke yi musu magana, don yana so ya saki Yesu. 21Amma suka yi ta ƙwala ihu, suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!” 22Ya sāke faɗa musu, a faɗa ta uku, “Ta wane hali? Wane mugun abu ya yi? Ai, ban sami dalilin kisa a gare shi ba. Saboda haka, zan yi masa bulala in sake shi.” 23Amma suka yi ta matsa lamba, suna ɗaga murya, suna cewa a gicciye shi, har surutunsu ya yi rinjaye. 24Sai Bilatus ya zartar da hukunci a biya musu bukata. 25Ya kuwa sakar musu wanda suka roƙa, wato, wanda aka jefa a kurkuku a kan laifin tawaye da kuma kisankai. Amma ya ba da Yesu, su yi masa abin da suke so.
An Gicciye Yesu
(Mat 27.32-44; Mar 15.21-32; Yah 19.17-27)
26Suna tafiya da Yesu yake nan, sai suka cafke wani, mai suna Saminu Bakurane, yana zuwa daga ƙauye, suka ɗora masa gicciye, yă ɗauka ya bi Yesu. 27Sai taron mutane masu yawan gaske suka bi shi, da waɗansu mata da suke kuka, suke kuma gunji saboda shi. 28Amma Yesu ya juya gare su, ya ce, “Ya ku matan Urushalima, ku bar yi mini kuka, sai dai ku yi wa kanku da kuma 'ya'yanku, 29don lokaci na zuwa da za su ce, ‘Albarka tā tabbata ga matan da suke bakararru, waɗanda ba su taɓa haihuwa ba, waɗanda kuma ba a taɓa shan mamansu ba.’ 30#Yush 10.8; W.Yah 6.16 Sa'an nan ne za su fara ce wa manyan duwatsu, ‘Ku faɗo a kanmu,’ su kuma ce da tsaunuka, ‘Ku binne mu.’ 31In fa irin abubuwan nan suna faruwa ga ɗanye, yaya zai zama ga ƙeƙasasshe?”
32Waɗansu mutum biyu kuma masu laifi, aka kai su a kashe su tare da shi. 33Da suka isa wurin da ake ce da shi Ƙoƙwan Kai, nan suka gicciye shi, da kuma masu laifin nan, ɗaya a damansa, ɗaya a hagun. 34#Zab 22.18 Sai Yesu ya ce, “Ya Uba, ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa, suna kuri'a a kansu. 35#Zab 22.7 Mutane da suke tsaitsaye, suna kallo. Shugabanni kuma suka yi masa ba'a, suka ce, “Ya ceci waɗansu, to, ya ceci kansa mana, in shi ne Almasihu na Allah zaɓaɓɓensa!” 36#Zab 69.21 Soja kuma suka yi masa ba'a, suka matso, suka miƙa masa ruwan tsami, 37suna cewa, “In kai ne Sarkin Yahudawa, to, ka cece kanka mana!” 38Sama da shi kuma aka yi wani rubutu cewa, “Wannan shi ne Sarkin Yahudawa.”
39Sai ɗaya daga cikin masu laifin da aka gicciye ya yi masa baƙar magana ya ce, “Shin, ba kai ne Almasihu ba? To, ceci kanku mana, duk da mu!” 40Amma ɗayan ya amsa, ya kwaɓe shi, ya ce, “Kai ko tsoron Allah ma ba ka yi, kai, da yake hukuncinka daidai da nasa? 41Mu kam, daidai aka yi mana, don hakika sakamakon aikinmu muka samu, amma mutumin nan bai yi wani laifi ba.” 42Ya kuma ce, “Ya Yesu, ka tuna da ni, sa'ad da ka shiga sarautarka.” 43Yesu ya ce masa, “Hakika, ina gaya maka, yau ma za ka kasance tare da ni a Firdausi.”
Mutuwar Yesu
(Mat 27.45-56; Mar 15.33-41; Yah 19.28-30)
44 #
Fit 26.31-33
To, wajen tsakar rana ne kuwa, sai duhu ya rufe ƙasa duka, har zuwa ƙarfe uku na yamma. 45Hasken rana ya dushe. Labulen da yake cikin Haikali ya tsage gida biyu. 46#Zab 31.5 Sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Ya Uba, na sa ruhuna a ikonka.” Da ya faɗi haka kuwa, sai ya cika. 47Sa'ad da jarumin ya ga abin da ya gudana, sai ya girmama Allah ya ce, “Hakika mutumin nan marar laifi ne!” 48Sa'ad da duk taro masu yawa, waɗanda suka zo kallo suka ga abin da ya faru, suka koma, suna bugun ƙirjinsu. 49#Luk 8.2,3 Amma duk idon sani, da kuma matan da suka biyo shi, tun daga ƙasar Galili, suka tsaya daga nesa, suna duban waɗannan abubuwa.
Jana'izar Yesu
(Mat 27.57-61; Mar 15.42-47; Yah 19.38-42)
50To, akwai wani mutum mai suna Yusufu, mutumin Arimatiya, wani garin Yahudawa, shi ɗan majalisa ne, nagari ne, adali kuma. 51Shi kuwa dā ma bai yarda da shawararsu, da kuma abin da suka yi ba, yana kuwa sauraron bayyanar Mulkin Allah. 52Shi ne ya tafi wurin Bilatus, ya roƙa a ba shi jikin Yesu. 53Sai ya sauko da shi, ya sa shi a likkafanin lilin, ya sa shi a wani kabari da aka fafe dutse aka yi, wanda ba a taɓa sa kowa ba. 54Ran nan kuwa ranar shiri ce, Asabar kuma ta doso. 55Matan nan kuwa da suka zo tare da shi daga ƙasar Galili, suka bi baya, suka duba kabarin da yadda kuma aka sa jikinsa. 56#Fit 20.10; M.Sh 5.14 Sai suka koma, suka shirya kayan ƙanshi da man shafawa.
Ran Asabar kuwa, sai suka huta bisa ga umarni.
Currently Selected:
Luk 23: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

: