Luk 3
3
Wa'azin Yahaya Maibaftisma
(Mat 3.1-12; Mar 1.1-8; Yah 1.19-28)
1A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tibariyas, Buntus Bilatus yana mulkin Yahudiya, Hirudus yana sarautar Galili, ɗan'uwansa Filibus yana sarauta Ituriya da Tarakunitas, Lisaniyas kuma yana sarautar Abiliya, 2a zamanin da Hanana da Kayafa suke manyan firistoci, Maganar Allah ta zaike wa Yahaya ɗan Zakariya a jeji. 3Sai ya zaga duk lardin bakin Kogin Urdun, yana wa'azi, cewa mutane su tuba a yi musu baftisma, domin a gafarta musu zunubansu, 4#Ish 40.3-5yadda yake a rubuce a Littafin Annabi Ishaya cewa,
“Muryar mai kira a jeji tana cewa,
Ku shirya wa Ubangiji tafarki,
Ku miƙe hanyoyinsa,
5Za a cike kowane kwari,
Kowane dutse da kowane tsauni za a baje su.
Za a miƙe karkatattun wurare,
Za a bi da hanyoyin da ba su biyu ba.
6Dukkan 'yan adam kuma za su ga ceton Allah.”
7 #
Mat 12.34; 23.33 Saboda haka, Yahaya ya ce wa taron jama'ar da yake zuwa domin ya yi musu baftisma, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa fushin nan mai zuwa? 8#Yah 8.33 Ku yi aikin da zai nuna tubanku, kada ma ku ko fara cewa a ranku Ibrahim ne ubanku. Ina dai gaya muku Allah yana da iko ya halitta wa Ibrahim 'ya'ya daga duwatsun nan. 9#Mat 7.19 Ko yanzu ma an ɗora bakin gatari a gindin itatuwa. Saboda haka duk itacen da bai yi 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare shi, a jefa a wuta.”
10Sai taron suka tambaye shi suka ce, “Me za mu yi ke nan?” 11Ya amsa musu ya ce, “Duk mai taguwa biyu, ya raba da marar ita, mai abinci ma haka.” 12#Luk 7.29 Masu karɓar haraji ma suka zo a yi musu baftisma, suka ce masa, “Malam, me za mu yi?” 13Ya ce musu, “Kada ku karɓi fiye da abin da aka umarce ku.” 14Waɗansu soja ma suka tambaye shi, “To, mu fa, me za mu yi?” Sai ya ce musu, “Kada ku yi wa kowa ƙwace ko ƙazafi. Ku dai dangana da albashinku.”
15Da yake mutane duk sun zaƙu, kowa yana wuswasi a ransa a game da Yahaya, ko watakila shi ne Almasihu, 16sai Yahaya ya amsa wa dukansu ya ce, “Ni kam, da ruwa nake yi muku baftisma, amma wani yana zuwa wanda ya fi ni girma, wanda ko maɓallin takalminsa ma ban isa in ɓalle ba. Shi ne zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta. 17Ƙwaryar shiƙarsa tana hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai sarai, ya taro alkama ya sa a rumbunsa, amma ɓuntun sai ya ƙone shi a wuta marar mutuwa.”
18Ta haka, da waɗansu gargaɗi masu yawa, Yahaya ya yi wa jama'a bishara. 19#Mat 14.3,4; Mar 6.17,18 Amma sarki Hirudus, wanda Yahaya ya tsawata wa a kan maganar Hirudiya, matar ɗan'uwansa, da kuma dukan mugayen ayyukan da ya yi, 20sai ya ƙara da kulle Yahaya a kurkuku.
An Yi wa Yesu Baftisma
(Mat 3.13-17; Mar 1.9-11)
21To, da aka yi wa dukan mutane baftisma, Yesu ma aka yi masa baftisma, yana addu'a ke nan, sai sama ta dāre, 22#Far 22.2; Zab 2.7; Ish 42.1; Mat 3.17; Mar 1.11; Luk 9.35 Ruhu Mai Tsarki ya sauko masa da wata kama, kamar kurciya. Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Kai ne Ɗana ƙaunataccena, ina farin ciki da kai ƙwarai,”
Asalin Yesu
(Mat 1.1-17)
23Yesu kuwa sa'ad da ya fara koyarwa, yana da shekara wajen talatin. An ɗauke shi a kan, wai shi ɗan Yusufu ne, wanda yake ɗan Heli, 24Heli ɗan Matat, Matat ɗan Lawi, Lawi ɗan Malki, Malki ɗan Yanna, Yanna ɗan Yusufu, 25Yusufu ɗan Matatiya, Matatiya ɗan Amos, Amos ɗan Nahum, Nahum ɗan Azaliya, Azaliya ɗan Najaya, 26Najaya ɗan Ma'ata, Ma'ata ɗan Matatiya, Matatiya ɗan Shimeya, Shimeya ɗan Yusufu, Yusufu ɗan Yahuza, 27Yahuza ɗan Yowana, Yowana ɗan Refaya, Refaya ɗan Zarubabel, Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, Sheyaltiyel ɗan Niri, 28Niri ɗan Malki, Malki ɗan Addi, Addi ɗan Kosama, Kosama ɗan Almadama, Almadama ɗan Er, 29Er ɗan Yosi, Yosi ɗan Eliyezer, Eliyezar ɗan Yorima, Yorima ɗan Matat, Matat ɗan Lawi, 30Lawi ɗan Saminu, Saminu ɗan Yahuza, Yahuza ɗan Yusufu, Yusufu ɗan Yonana, Yonana ɗan Eliyakim, 31Eliyakim ɗan Malaya, Malaya ɗan Mainana, Mainana ɗan Matata, Matata ɗan Natan, Natan ɗan Dawuda, 32Dawuda ɗan Yesse, Yesse ɗan Obida, Obida ɗan Bo'aza, Bo'aza ɗan Salmon, Salmon ɗan Nashon, 33Nashon ɗan Amminadab, Amminadab ɗan Aram, Aram ɗan Hesruna, Hesruna ɗan Feresa, Feresa ɗan Yahuza, 34Yahuza ɗan Yakubu, Yakubu ɗan Ishaku, Ishaku ɗan Ibrahim, Ibrahim ɗan Tera, Tera ɗan Nahor, 35Nahor ɗan Serug, Serug ɗan Reyu, Reyu ɗan Feleg, Feleg ɗan Eber, Eber ɗan Shela, 36Shela ɗan Kenan, Kenan ɗan Arfakshad, Arfakshad ɗan Shem, Shem ɗan Nuhu, Nuhu ɗan Lamek, 37Lamek ɗan Metusela, Metusela ɗan Anuhu, Anuhu ɗan Yared, Yared ɗan Mahalel, Mahalel ɗan Kenan, 38Kenan ɗan Enosh, Enosh ɗan Shitu, Shitu ɗan Adamu, Adamu kuma na Allah.
Currently Selected:
Luk 3: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

: