Luk 7:21-22
Luk 7:21-22 HAU
Nan take Yesu ya warkar da mutane da yawa daga rashin lafiyarsu da cuce-cucensu da kuma baƙaƙen aljannu. Makafi da yawa kuma ya yi musu baiwar gani. Sai ya amsa musu ya ce, “Ku je ku gaya wa Yahaya abin da kuka ji da abin da kuka gani. Makafi na samun gani, guragu na tafiya, ana tsarkake kutare, kurame na ji, ana ta da matattu, ana kuma yi wa matalauta bishara.