Luk 7
7
Yesu Ya Warkar da Bawan Wani Jarumi
(Mat 8.5-13)
1Bayan da Yesu ya ƙare jawabinsa duka a gaban jama'a, ya shiga Kafarnahum. 2To, sai bawan wani jarumi, wanda Ubangijinsa yake jin daɗinsa, ya yi rashin lafiya, har ya kai ga bakin mutuwa. 3Da jarumin ɗin ya ji labarin Yesu, sai ya aiki waɗansu shugabannin Yahudawa wurinsa, su roƙe shi ya zo ya warkar da bawa nasa. 4Da suka isa wurin Yesu sai suka roƙe shi ƙwarai suka ce, “Ai, ya cancanci a yi masa haka, 5don yana ƙaunar jama'armu, shi ne ma ya gina mana majami'armu.” 6Sai Yesu ya tafi tare da su. Da ya matso kusa da gidan, sai jarumin ɗin ya aiki aminansa wurinsa su ce masa, “Ya Ubangiji, kada ka wahalar da kanka. Ban ma isa har ka zo gidana ba. 7Shi ya sa ban ga ma na isa in zo wurinka ba, amma kă yi magana kawai, yarona kuwa sai ya warke. 8Don ni ma a hannun wani nake, da kuma soja a hannuna, in ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai ya je, wani kuwa in ce masa, ‘Zo,’ sai ya zo, in ce wa bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai ya yi.” 9Da Yesu ya ji haka, ya yi mamakinsa, ya kuma juya ya ce wa taron da suke biye da shi, “Ina gaya muku, ko a cikin Isra'ila ban taɓa samun bangaskiya mai ƙarfi irin wannan ba.” 10Da waɗanda aka aika suka koma gidan, suka sami bawan garau.
Yesu Ya Tā da Ɗan Mace wadda Mijinta Ya Mutu
11Ba da daɗewa ba, Yesu ya tafi wani gari, wai shi Nayin, almajiransa da kuma babban taro suka tafi da shi. 12Ya kusaci ƙofar garin ke nan, sai ga wani mamaci ana ɗauke da shi, shi kaɗai ne wajen uwa tasa, mijinta kuwa ya mutu. Mutanen gari da yawa sun rako ta. 13Da Ubangiji ya gan ta, ya ji tausayinta, ya kuma ce mata, “Daina kuka.” 14Sa'an nan ya matso, ya taɓa makarar, masu ɗauka kuma suka tsaya cik. Sai Yesu ya ce, “Samari, na ce maka ka tashi.” 15Mamacin ya tashi zaune, ya fara magana. Yesu kuwa ya ba da shi ga uwa tasa. 16Sai tsoro ya kama su duka, suka ɗaukaka Allah suna cewa, “Lalle, wani annabi mai girma ya bayyana a cikinmu,” da kuma, “Allah ya kula da jama'arsa.” 17Wannan labarin nasa kuwa ya bazu a dukan ƙasar Yahudiya da kewayenta.
'Yan Saƙo daga Yahaya Maibaftisma
(Mat 11.2-19)
18Sai almajiran Yahaya suka gaya masa dukan abubuwan nan. 19Sai Yahaya ya kira almajiransa biyu, ya aike su gun Ubangiji yana tambaya, “Kai ne mai zuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?” 20Da mutanen nan suka isa wurinsa, suka ce, “Yahaya Maibaftisma ne ya aiko mu gare ka, yana tambaya, ‘Kai ne mai zuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?’ ” 21Nan take Yesu ya warkar da mutane da yawa daga rashin lafiyarsu da cuce-cucensu da kuma baƙaƙen aljannu. Makafi da yawa kuma ya yi musu baiwar gani. 22#Ish 35.5,6; Ish 61.1 Sai ya amsa musu ya ce, “Ku je ku gaya wa Yahaya abin da kuka ji da abin da kuka gani. Makafi na samun gani, guragu na tafiya, ana tsarkake kutare, kurame na ji, ana ta da matattu, ana kuma yi wa matalauta bishara. 23Albarka tā tabbata ga wanda ba ya tuntuɓe sabili da ni.”
24Baya jakadun Yahaya sun tafi, sai Yesu ya fara yi wa taro maganar Yahaya, ya ce, “Kallon me kuka je yi a jeji? Kyauron da iska take kaɗawa? 25To, kallon me kuka je yi? Wani mai adon alharini? Ai kuwa, masu adon gaske, masu zaman annashuwa, a fāda suke. 26To, kallon me kuka je yi? Annabi? Hakika, ina gaya muku, har ya fi annabi nesa. 27#Mal 3.1 Wannan shi ne wanda labarinsa yake rubuce cewa,
“ ‘Ga shi, na aiko manzona ya riga ka gaba,
Wanda zai shirya maka hanya gabaninka.’
28“Ina gaya muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yahaya girma. Duk da haka wanda ya fi ƙasƙanta a Mulkin Allah ya fi shi.” 29#Mat 21.32; Luk 3.12 Da duk jama'a da masu karɓar haraji suka ji haka, suka tabbata Allah mai adalci ne, aka yi musu baftisma da baftismar Yahaya. 30Amma Farisiyawa da masanan Attaura suka shure abin da Allah yake nufinsu da shi, da yake sun ƙi ya yi musu baftisma.
31“To, da me zan kwatanta mutanen zamanin nan? Waɗanne iri ne su? 32Kamar yara suke da suke zaune a bakin kasuwa, suna kiran juna, suna cewa,
“ ‘Mun busa muku sarewa, ba ku yi rawa ba,
Mun yi makoki, ba ku yi kuka ba.’
33“Ga shi, Yahaya Maibaftisma ya zo, ba ya cin gurasa, ba ya shan ruwan inabi, amma kuna cewa, ‘Ai, yana da iska.’ 34Ga Ɗan Mutum ya zo, yana ci yana sha, kuna kuma cewa, ‘Ga mai haɗama, mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi!’ 35Duk da haka hikimar Allah, ta dukkan aikinta ne ake tabbatar da gaskiya tata.”
Yesu a Gidan Saminu Bafarisiye
36Wani Bafarisiye ya kira shi cin abinci. Sai ya shiga gidan Bafarisiyen, ya ƙishingiɗa wurin cin abincin. 37#Mat 26.7; Mar 14.3; Yah 12.3Sai ga wata matar garin, mai zunubi, da ta ji Yesu na cin abinci a gidan Bafarisiyen, ta kawo wani ɗan tandu na man ƙanshi, 38ta tsaya a bayansa a wajen ƙafafunsa, tana kuka. Sai hawayenta ya fara zuba a ƙafafunsa, ta goge su da gashinta, ta yi ta sumbantarsu, ta shafa musu man ƙanshin. 39To, da Bafarisiyen da ya kira shi ya ga haka, sai ya ce a ransa, “Da mutumin nan annabi ne, da ya san ko wace ce, da kuma ko wace irin mace ce wannan da yake taɓa shi, don mai zunubi ce.” 40Yesu ya amsa ya ce, “Saminu, ina da magana da kai.” Sai shi kuma ya ce, “Malam, sai ka faɗa.” 41Yesu ya ce, “Wani yana bin mutum biyu bashi, ɗaya dinari ɗari biyar, ɗayan kuma hamsin. 42Da suka gagara biya, sai ya yafe musu dukansu biyu. To, a cikinsu wa zai fi ƙaunarsa?” 43Saminu ya amsa masa ya ce, “A ganina, wanda ya yafe wa mai yawa.” Sai ya ce masa “Ka faɗa daidai.” 44Da ya waiwaya wajen matar, ya ce wa Saminu. “Ka ga matan nan? Na shigo gidanka, ba ka ba ni ruwan wanke ƙafa ba, amma ita ta zub da hawayenta a ƙafafuna, ta kuma goge su da gashinta. 45Kai ba ka sumbance ni ba, ita kuwa, tun shigowata nan ba ta daina sumbantar ƙafafuna ba. 46Ba ka shafa mini mai a ka ba, amma ita ta shafa man ƙanshi a ƙafafuna. 47Saboda haka ina gaya maka, zunubanta masu yawan nan duk an gafarta mata, domin ta yi ƙauna mai yawa. Wanda aka gafarta wa kaɗan kuwa, ƙauna kaɗan yake yi.” 48Sai ya ce mata, “An gafarta miki zunubanki.” 49Masu ci tare da shi kuwa suka fara ce wa juna, “Wannan kuwa wane ne wanda har yake gafarta zunubai?” 50Sai Yesu ya ce wa matar, “Bangaskiyarki ta cece ki. Ki sauka lafiya.”
Currently Selected:
Luk 7: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

: