1
Yohanna 1:12
Sabon Rai Don Kowa 2020
Duk da haka dukan waɗanda suka karɓe shi, ga waɗanda suka gaskata a sunansa, ya ba su iko su zama ’ya’yan Allah
Compara
Explorar Yohanna 1:12
2
Yohanna 1:1
Tun farar farawa akwai Kalma, Kalman kuwa yana nan tare da Allah, Kalman kuwa Allah ne.
Explorar Yohanna 1:1
3
Yohanna 1:5
Hasken yana haskakawa cikin duhu, amma duhun bai rinjaye shi ba.
Explorar Yohanna 1:5
4
Yohanna 1:14
Kalman ya zama mutum, ya kuwa zauna a cikinmu. Muka ga ɗaukakarsa, ɗaukaka ta wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaici, wanda ya zo daga wurin Uba, cike da alheri da gaskiya.
Explorar Yohanna 1:14
5
Yohanna 1:3-4
Ta wurin Kalman ne aka halicci dukan abubuwa. In ba tare da shi ba, babu abin da aka yi wanda aka yi. A cikinsa rai ya kasance, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane.
Explorar Yohanna 1:3-4
6
Yohanna 1:29
Kashegari Yohanna ya ga Yesu yana zuwa wajensa sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah mai ɗauke zunubin duniya!
Explorar Yohanna 1:29
7
Yohanna 1:10-11
Yana a duniya, kuma ko da yake an yi duniya ta wurinsa ne, duniya ba tă gane shi ba. Ya zo wurin abin da yake nasa, amma nasa ɗin ba su karɓe shi ba.
Explorar Yohanna 1:10-11
8
Yohanna 1:9
Haske na gaskiya da yake ba da haske ga kowane mutum mai shigowa duniya.
Explorar Yohanna 1:9
9
Yohanna 1:17
Gama an ba da doka ta wurin Musa; alheri da gaskiya kuwa sun zo ne ta wurin Yesu Kiristi.
Explorar Yohanna 1:17
Inici
La Bíblia
Plans
Vídeos