1
Luka 17:19
Sabon Rai Don Kowa 2020
Sai ya ce masa, “Tashi, ka yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai.”
Compara
Explorar Luka 17:19
2
Luka 17:4
In ya yi maka laifi sau bakwai a rana ɗaya, ya kuma dawo sau bakwai ɗin a wurinka, yana cewa, ‘Na tuba,’ sai ka gafarta masa.”
Explorar Luka 17:4
3
Luka 17:15-16
Da ɗayansu ya ga ya warke, sai ya koma, yana yabon Allah da babbar murya. Ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, ya gode masa. Shi kuwa mutumin Samariya ne.
Explorar Luka 17:15-16
4
Luka 17:3
Saboda haka, ku lura da kanku. “In ɗan’uwanka ya yi zunubi, ka kwaɓe shi. In ya tuba, ka gafarta masa.
Explorar Luka 17:3
5
Luka 17:17
Yesu ya yi tambaya ya ce, “Ba duka goma ne aka tsabtacce ba? Ina sauran taran?
Explorar Luka 17:17
6
Luka 17:6
Ya amsa musu ya ce, “In kuna da bangaskiya da take ƙanƙani kamar ƙwayar mustad, kuna iya ce wa wannan itacen durumi, ‘Ka tumɓuke daga nan, ka dasu a cikin teku.’ Zai kuwa yi muku biyayya.
Explorar Luka 17:6
7
Luka 17:33
Duk wanda yake so ya ceci ransa, zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa, zai cece shi.
Explorar Luka 17:33
8
Luka 17:1-2
Yesu ya ce wa almajiransa, “Dole ne a sami abubuwan da suke sa mutane su yi zunubi, amma kaiton mutumin nan wanda suke zuwa ta wurinsa. Gwamma a ɗaura dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi cikin teku, da ya sa ɗaya daga cikin ƙananan yaran nan ya yi zunubi.
Explorar Luka 17:1-2
9
Luka 17:26-27
“Daidai kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka zai zama a zamanin Ɗan Mutum. Mutane suna ci, suna sha, suna aurayya, ana kuma ba da su ga aure, har ranar da Nuhu ya shiga jirgin. Sa’an nan ambaliyar ruwan ya sauka, ya hallaka su duka.
Explorar Luka 17:26-27
Inici
La Bíblia
Plans
Vídeos