Farawa 24:14

Farawa 24:14 SRK

Bari yă zama sa’ad da na ce wa wata yarinya, ‘Ina roƙonki ki saukar da tulunki domin in sha,’ in ta ce, ‘Ka sha, zan kuma ba wa raƙumanka ma’; bari tă zama ita ce ka zaɓa wa bawanka Ishaku. Ta haka zan san cewa ka nuna wa maigidana alheri.”