Luka 22

22
Yahuda ya yarda ya bashe Yesu
(Mattiyu 26.1-5,14,16; Markus 14.1,2,10,11; Yohanna 11.45-53)
1Yanzu fa, Bikin Burodi Marar Yistin da ake kira Bikin Ƙetarewa ya yi kusa, 2manyan firistoci da malaman dokoki kuma suna neman yadda za su kashe Yesu a ɓoye, don suna tsoron mutane. 3Shaiɗan kuwa ya shiga Yahuda, wanda ake kira Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun. 4Sai Yahuda ya je ya tattauna da manyan firistoci, da ma’aikatan ’yan gadin haikali, a kan yadda zai ba da Yesu a gare su. 5Suka kuwa yi murna, suka yarda su ba shi kuɗi. 6Ya ko yarda, ya fara neman zarafin da zai ba da Yesu a gare su, sa’ad da taro ba sa nan tare da shi.
Abincin yamma na ƙarshe
(Mattiyu 26.17-25; Markus 14.12-21; Yohanna 13.21-30)
7Sai ranar Bikin Burodi Marar Yisti ta kewayo, wato, ranar hadayar ɗan ragon kafara na Bikin Ƙetarewa. 8Sai Yesu ya aiki Bitrus da Yohanna, ya ce musu, “Ku je ku yi shirye-shiryen Bikin Ƙetarewar da za mu ci.”
9Suka tambaye shi suka ce, “Ina kake so mu je mu yi shirin?”
10Ya amsa ya ce, “Sa’ad da kuka shiga cikin gari, za ku sadu da wani mutum yana ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi zuwa gidan da zai shiga. 11Ku ce wa maigidan, Malam ya aike mu mu ce maka, ‘Ina ɗakin baƙi, inda ni da almajiraina za mu ci abincin Bikin Ƙetarewa?’ 12Zai nuna muku wani babban ɗakin sama a shirye. Nan za ku yi shirin.”
13Sai suka tafi, suka kuma iske kome kamar yadda Yesu ya faɗa musu. Sai suka shirya Bikin Ƙetarewa.
(Mattiyu 26.26-30; Markus 14.22-26; 1 Korintiyawa 11.23-25)
14Da lokaci ya yi, sai Yesu ya zauna tare da manzanninsa don cin abinci. 15Sai ya ce musu, “Na yi marmari ƙwarai don in ci wannan Bikin Ƙetarewa tare da ku, kafin in sha wahala. 16Ina dai gaya muku, ba zan ƙara cinsa ba, sai ya sami cika a mulkin Allah.”
17Bayan ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya yi godiya, sai ya ce, “Ku karɓa, ku rarraba wa junanku. 18Ina dai gaya muku, ba zan ƙara sha daga ’ya’yan inabi ba, sai mulkin Allah ya zo.”
19Sai ya ɗauki burodi ya yi godiya, ya kakkarya ya ba su, da cewa, “Wannan jikina ne, da aka bayar dominku. Ku riƙa yin haka don tunawa da ni.”
20Haka kuma, bayan abincin, ya ɗauki kwaf ruwan inabi ya ce, “Wannan kwaf ruwan inabi shi ne, na sabon alkawari cikin jinina, da aka zubar dominku. 21Amma hannun wanda zai ci amanata, yana cin abincin tare da ni. 22Ɗan Mutum zai mutu kamar yadda aka ƙaddara, amma kaiton mutumin da zai bashe shi.” 23Sai suka fara tambayar junansu, ko wane ne a cikinsu zai yi wannan.
24Gardama ta tashi a tsakaninsu, a kan ko wane ne a cikinsu ya fi girma. 25Yesu ya ce musu, “Sarakunan Al’ummai suna nuna iko a kan mutanensu, kuma waɗanda suke nuna iko a kansu, suna kiran kansu Masu Taimakon mutane. 26Amma ku, kada ku zama haka. A maimakon haka, sai dai wanda ya fi girma a cikinku, ya zama kamar wanda ya fi ƙanƙanta, wanda kuma ke mulki, ya zama kamar mai hidima. 27Wane ne ya fi girma? Wanda yake zaune a tebur ne, ko kuma shi da yake yin hidima? Ashe, ba wanda yake zaune a tebur ba ne? Amma ga ni, ni mai yin hidima ne a cikinku. 28Ku ne kuka tsaya tare da ni a gwaje-gwajen da na sha. 29Daidai kamar yadda Ubana ya ba ni mulki, haka ni ma nake ba ku. 30Saboda ku ci, ku sha a teburina a cikin mulkina. Kuma ku zauna a kan gadon sarauta, ku yi wa kabilu goma sha biyu na Isra’ila shari’a.
(Mattiyu 26.31-35; Markus 14.27-31; Yohanna 13.36-38)
31 “Siman, Siman, Shaiɗan ya nemi izini ya sheƙe ka # 22.31 Girik yana da ku ne a nan kamar alkama. 32Amma na yi maka addu’a, Siman, domin kada bangaskiyarka ta kāsa. Bayan ka juyo, ka ƙarfafa ’yan’uwanka.”
33Amma ya amsa ya ce, “Ubangiji, ina a shirye in tafi tare da kai har kurkuku, ko mutuwa ma.”
34Yesu ya ce, “Ina gaya maka Bitrus, kafin zakara ya yi cara yau, za ka yi mūsun sanina sau uku.”
35Sai Yesu ya tambaye, su ya ce, “Lokacin da na aike ku ba tare da jakar kuɗi, ko jaka, ko takalma ba, kun rasa wani abu?”
Suka amsa, “Babu.”
36Ya ce musu, “Amma yanzu, in kuna da jakar kuɗi, ko jaka, ku ɗauka. In kuma ba ku da takobi, ku sayar da rigarku, ku saya. 37A rubuce yake cewa, ‘An lissafta shi tare da masu zunubi.’ Ina kuwa gaya muku, dole wannan ya cika a kaina. I, abin da aka rubuta a kaina yana kusan cikawa.”
38Almajiran suka ce, “Duba Ubangiji, ga takuba biyu.”
Yesu ya ce, “Ya isa.”
Yesu ya yi addu’a a Dutsen Zaitun
(Mattiyu 26.36-46; Markus 14.32-42)
39Yesu ya fita zuwa Dutsen Zaitun kamar yadda ya saba, almajiransa kuma suka bi shi. 40Da ya kai wurin, sai ya ce musu, “Ku yi addu’a don kada ku fāɗi cikin jarraba.” 41Sai ya janye daga wurinsu, misalin nisan jifa, ya durƙusa a ƙasa ya yi addu’a, 42“Uba, in ka yarda, ka ɗauke mini wannan kwaf, amma ba nufina ba, sai dai naka.” 43Wani mala’ika daga sama ya bayyana gare shi, ya ƙarfafa shi. 44Domin tsananin azaba, sai ya ƙara himma cikin addu’a, zuffansa kuma na ɗigowa ƙasa kamar jini.
45Da ya tashi daga addu’a, ya koma inda almajiransa suke, sai ya iske su suna barci, daga gajiyar baƙin ciki. 46Ya tambaye su, “Don me kuke barci? Ku tashi ku yi addu’a, don kada ku fāɗi cikin jarraba.”
An kama Yesu
(Mattiyu 26.47-56; Markus 14.43-50; Yohanna 18.3-11)
47Yana cikin magana sai ga taro sun zo. Mutumin nan da ake kira Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun, shi ya bi da su. Sai ya matso kusa da Yesu don yă yi masa sumba. 48Amma Yesu ya tambaye shi ya ce, “Yahuda, ashe, da sumba za ka bashe Ɗan Mutum?”
49Da masu bin Yesu suka ga abin da zai faru, sai suka ce, “Ubangiji, mu yi sara da takubanmu ne?” 50Sai ɗayansu ya kai sara ga bawan babban firist, ya sare kunnen damansa.
51Amma Yesu ya amsa ya ce, “Kada a ƙara yin wannan!” Sai ya taɓa kunnen mutumin da aka sara, ya warkar da shi.
52Sai Yesu ya ce wa manyan firistoci, da ma’aikatan ’yan gadin haikali, da dattawa, waɗanda suka zo don su kama shi, “Ina jagoran wani tawaye ne, da za ku zo da takuba da sanduna? 53Kullum ina tare da ku a filin haikali, amma ba ku kama ni ba. Amma wannan ne sa’a naku, lokacin da duhu yake mulki.”
Bitrus ya yi mūsun sanin Yesu
(Mattiyu 26.57,58,67-75; Markus 14.53,54,66-72; Yohanna 18.12-18,25-27)
54Sai suka kama shi suka kai shi gidan babban firist. Bitrus ya bi su daga nesa. 55Amma da suka hura wuta a tsakiyar harabar gidan, kowa ya zauna, sai Bitrus ya zo ya zauna tare da su. 56Wata baiwa ta gan shi zaune kusa da wutar. Ta dube shi sosai sa’an nan, ta ce, “Ai, wannan mutum ma yana tare da shi.”
57Amma ya yi mūsu ya ce, “Mace, ban san shi ba!”
58Bayan ɗan lokaci kaɗan, wani dabam ya gan shi ya ce, “Kai ma ɗayansu ne.”
Bitrus ya amsa ya ce, “Kai, ba na cikinsu!”
59Bayan kamar sa’a ɗaya, sai wani mutum ya ce, “Ba shakka, mutumin nan ma yana tare da shi, don shi mutumin Galili ne.”
60Bitrus ya amsa ya ce, “Kai, ban ma san abin da kake magana a kai ba!” Yana cikin magana, sai zakara ya yi cara. 61Ubangiji kuma ya juya ya kafa wa Bitrus ido. Sai Bitrus ya tuna da maganar da Ubangiji ya ce masa, “Kafin zakara ya yi cara yau, za ka yi mūsun sanina sau uku.” 62Sai ya fita waje, ya yi kuka mai zafi.
Masu gadi sun yi wa Yesu ba’a
(Mattiyu 26.59-66; Markus 14.55-64; Yohanna 18.19-24)
63Mutanen da suke gadin Yesu suka fara masa ba’a da dūka. 64Suka rufe masa idanu suna tambaya cewa, “Ka yi annabci! Wa ya mare ka?” 65Suka kuma yi masa waɗansu baƙaƙen maganganu masu yawa.
Yesu a gaban Bilatus da Hiridus
66Da gari ya waye, sai majalisar dattawa na mutane, da manyan firistoci, da malaman dokoki, suka taru wuri ɗaya. Sai aka kawo Yesu a gabansu. 67Suka ce, “Ka faɗa mana, ko kai ne Kiristi?”
Yesu ya amsa ya ce, “Ko na gaya muku, ba za ku gaskata ni ba, 68in kuma na yi muku tambaya ba za ku iya ba ni amsa ba. 69Amma daga yanzu, Ɗan Mutum zai zauna a hannun dama na Allah Mai Iko.”
70Sai dukansu suka yi tambaya suka ce, “Wato, kai Ɗan Allah ke nan?”
Ya amsa ya ce, “Kun faɗa daidai, ni ne.”
71Sai suka ce, “Wace shaida kuma muke nema? Ai, mun ji abin da ya ce da bakinsa.”

S'ha seleccionat:

Luka 22: SRK

Subratllat

Comparteix

Copia

None

Vols que els teus subratllats es desin a tots els teus dispositius? Registra't o inicia sessió