Yah 10
10
Misali na Garken Tumaki
1“Lalle hakika, ina gaya muku, wanda bai shiga garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya haura ta wani gu, to, shi ɓarawo ne, ɗan fashi kuma. 2Wanda kuwa ya shiga ta ƙofar, makiyayin tumakin ne. 3Mai tsaron ƙofar yakan buɗe masa, tumakin kuma sukan saurari murya tasa, yakan kama sunan nasa tumaki, ya kai su waje. 4Bayan ya fitar da dukan nasa waje, sai ya shige gabansu, tumakin na biye da shi, domin sun san murya tasa. 5Ba za su bi baƙo ba, sai dai su guje shi, don ba su san muryar baƙo ba.” 6Yesu ya yi musu wannan misali, amma ba su gane abin da ya faɗa musu ba.
Yesu Ne Makiyayi Mai Kyau
7Don haka Yesu ya sāke ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, ni ne ƙofar tumakin. 8Duk waɗanda suka riga ni zuwa cewa, su ne ni, ɓarayi ne, 'yan fashi kuma, amma tumakin ba su kula da su ba. 9Ni ne ƙofar. Kowa ya shiga ta wurina zai sami ceto, ya kai ya kawo, ya kuma yi kiwo. 10Ɓarawo yakan zo ne kawai don sata da kisa da hallakarwa. Ni kuwa na zo ne domin su sami rai, su kuma same shi a yalwace. 11Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau kuwa shi ne mai ba da ransa domin tumakin. 12Wanda yake ɗan asako kuwa, ba makiyayin gaske ba, tumakin kuma ba nasa ba, da ganin kyarkeci ya doso, sai ya watsar da tumakin, ya yi ta kansa, kyarkeci kuwa ya sure waɗansu, ya fasa sauran. 13Ya gudu ne fa, don shi ɗan asako ne, ba abin da ya dame shi da tumakin. 14#Mat 11.27; Luk 10.22 Ni ne Makiyayi mai kyau. Na san nawa, nawa kuma sun san ni, 15kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uban. Ina ba da raina maimakon tumakin. 16Ina kuma da waɗansu tumaki da ba na wannan garke ba ne. Su ma lalle in kawo su, za su kuwa saurari muryata, su zama garke guda, makiyayi kuma guda. 17Domin wannan uba yake ƙaunata, domin ina ba da raina in ɗauko shi kuma. 18Ba mai karɓe mini rai, don kaina nake ba da shi. Ina da ikon ba da shi, ina da ikon ɗauko shi kuma. Na karɓo wannan umarni ne daga wurin Ubana.”
19Saboda maganan nan fa, sai rabuwa ta sāke shiga tsakanin Yahudawa. 20Da yawa daga cikinsu suka ce, “Ai, mai iska ne, haukansa kawai yake yi. Don me za ku saurare shi?” 21Waɗansu kuwa suka ce, “A'a, wannan magana, ai, ba ta mai iska ba ce. Ashe, iska tana iya buɗe wa makaho ido?”
Yahudawa Sun Ƙi Yesu
22Lokacin idin tsarkakewa ne kuwa a Urushalima, 23damuna ce kuma, Yesu kuwa na zagawa a Shirayin Sulemanu cikin Haikali, 24sai Yahudawa suka kewaye shi, suka ce masa, “Har yaushe za ka bar mu da shakka? In dai kai ne Almasihun, ka gaya mana a fili.” 25Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, na faɗa muku, ba ku gaskata ba. Ayyukan da nake yi da sunan Ubana, suke shaidata. 26Amma ku ba ku gaskata ba, domin ba kwa cikin tumakina. 27Tumakin nan nawa sukan saurari muryata, na san su, suna kuma bi na. 28Ina ba su rai madawwami, ba kuwa za su halaka ba har abada, ba kuma mai ƙwace su daga hannuna. 29Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba kuwa mai iya ƙwace su daga ikon Uban. 30Ni da Uba ɗaya muke.”
31Sai Yahudawa suka sāke ɗebo duwatsu su jajjefe shi. 32Yesu ya amsa musu ya ce, “Na nuna muku ayyuka nagari masu yawa daga wurin Uba, a kan wanne a cikinsu za ku jajjefe ni?” 33#L.Fir 24.16 Yahudawa suka amsa suka ce, “Ba don wani aiki nagari za mu jajjefe ka ba, sai don sāɓo, don kai, ga ka mutum, amma kana mai da kanka Allah.” 34#Zab 82.6 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba a rubuce yake a Shari'arku ba cewa, ‘Na ce ku alloli ne’? 35To, in waɗanda Maganar Allah ta zo musu ya ce da su alloli (Nassi kuwa ba ya tashi), 36kwa ce da wanda Uba ya keɓe, ya kuma aiko duniya, ‘Sāɓo kake,’ domin na ce, ‘Ni Ɗan Allah ne’? 37In ba ayyukan da Ubana yake yi nake yi ba, to, kada ku gaskata ni. 38Amma in su nake yi, ko ba ku gaskata ni ba, to, ku gaskata ayyukan, don ku sani, ku kuma gane, Uba na cikina, ni kuma ina cikin Uba.” 39Sai suka sāke ƙoƙarin kama shi, amma ya fita daga hannunsu.
40 #
Yah 1.28
Sa'an nan ya sāke komawa hayin Kogin Urdun, wurin da Yahaya ya fara yin baftisma, ya zauna a can, 41mutane kuwa da yawa suka zo wurinsa, sai suka riƙa cewa, “Hakika, Yahaya bai yi wata mu'ujiza ba, amma duk abin da ya faɗa game da mutumin nan gaskiya ne.” 42Nan fa mutane da yawa suka gaskata da shi.
S'ha seleccionat:
Yah 10: HAU
Subratllat
Comparteix
Copia
Vols que els teus subratllats es desin a tots els teus dispositius? Registra't o inicia sessió
@Bible Society of Nigeria 1979

: