Logo YouVersion
Îcone de recherche

Yah 13

13
Yesu Ya Wanke Ƙafafun Almajiransa
1Ana nan tun kafin Idin Ƙetarewa, da Yesu ya san lokacinsa ya yi da zai tashi daga wannan duniya ya koma wurin Uba, da yake ya ƙaunaci mutanensa da suke duniya, ya ƙaunace su har matuƙa. 2Ana cikin cin abincin dare, Iblis kuwa ya riga ya sa a zuciyar Yahuza Iskariyoti ɗan Saminu yă bāshe shi. 3Yesu kuwa, da yake ya san Uba ya sa kome a hannunsa, ya kuma sani daga wurin Allah ya fito, wurin Allah kuma zai koma, 4sai ya tashi daga cin abincin, ya ajiye mayafinsa, ya ɗauko ɗan zane ya yi ɗamara da shi. 5Sa'an nan ya zuba ruwa a daro, ya fara wanke ƙafafun almajiran, yana shafe su da abin da ya yi ɗamara da shi. 6Sai ya zo kan Bitrus, shi kuwa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ashe, kai ne za ka wanke mini ƙafa?” 7Yesu ya amsa ya ce, “Yanzu kam, ba ka san abin da nake yi ba, amma daga baya za ka fahimta.” 8Bitrus ya ce masa, “Wane ni! Ai, ba za ka wanke mini ƙafa ba har abada!” Yesu ya amsa masa ya ce, “In ban wanke maka ba, ba ka da rabo a gare ni.” 9Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ba ma ƙafafuna kaɗai ba, har ma da hannuwana da kaina!” 10Yesu ya ce masa, “Wanda ya yi wanka ba ya bukatar wanke kome, sai ƙafafunsa kawai, domin ya riga ya tsarkaka sarai. Ku ma tsarkakakku ne, amma ba dukanku ne ba.” 11Don ya san wanda zai bāshe shi, shi ya sa ya ce, “Ba dukanku ne tsarkakakku ba.”
12 # Luk 22.27 Bayan ya wanke ƙafafunsu, ya yafa mayafinsa, sai ya sāke kishingiɗa, ya ce musu, “Kun gane abin da na yi muku? 13Kuna kirana Malam, da kuma Ubangiji. Daidai ne kuwa, don haka nake. 14Tun da yake ni Ubangijinku da kuma Malaminku, har na wanke muku ƙafa, ashe, ku ma wajibi ne ku wanke wa juna. 15Na yi muku ishara domin ku ma ku yi yadda na yi muku 16#Mat 10.24; Luk 6.40; Yah 15.20 Lalle hakika, ina gaya muku, bawa ba ya fin ubangijinsa, manzo kuma ba ya fin wanda ya aiko shi. 17In dai kun san wannan, kuna kuma aikatawa, ku masu farin ciki ne. 18#Zab 41.9 Ba dukanku nake nufi ba. Na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa duk domin a cika Nassi ne cewa, ‘Wanda yake cin abincina ya tasar mini.’ 19Tun yanzu zan sanar da ku abu tun bai faru ba, domin sa'ad da ya faru ku ba da gaskiya ni ne shi. 20#Mat 10.40; Mar 9.37; Luk 9.48; 10.16 Lalle hakika, ina gaya muku, wanda ya yi na'am da duk wanda na aiko, ya yi na'am da ni ke nan. Wanda ya yi na'am da ni kuwa, to, ya yi na'am da wanda ya aiko ni.”
Yesu Ya Ce Za a Bāshe Shi
(Mat 26.20-25; Mar 14.17-21; Luk 22.21-23)
21Bayan da Yesu ya faɗi haka, ya ji nauyi a ransa, ya yi shaida ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bāshe ni.” 22Sai almajiran suka duddubi juna, suka rasa da wanda yake. 23Wani daga cikin almajiransa kuwa, wanda Yesu yake ƙauna, yana kishingiɗe gab da Yesu. 24Sai Bitrus ya alamta masa ya ce, “Gaya mana, da wa yake?” 25Shi kuwa da yake kishingiɗe haka gab da Yesu ya karkata, ya ce masa, “Ya Ubangiji, wane ne?” 26Sai Yesu ya amsa ya ce, “Shi ne wanda zan tsoma 'yar lomar nan in ba shi.” Da ya tsoma 'yar lomar kuwa, sai ya ba Yahuza, Ɗan Saminu Iskariyoti. 27Da karɓar 'yar loman nan Shaiɗan ya shige shi. Yesu ya ce masa, “Yi abin da za ka yi, maza.” 28Amma cikin waɗanda suke cin abinci, ba wanda ya san dalilin da ya sa Yesu ya faɗa masa haka. 29Har waɗansu ma sun yi zaton Yesu ya ce masa ya yi musu sayayyar idi ne, ko kuwa ya ba gajiyayyu wani abu, don Yahuza ne yake riƙe da jakar kuɗinsu. 30Shi kuwa da karɓar 'yar lomar, sai ya fita, da dare ne kuwa.
Sabon Umarni
31Bayan ya fita kuma sai Yesu ya ce, “Yanzu ne aka ɗaukaka Ɗan Mutum, aka kuma ɗaukaka Allah ta wurinsa. 32Allah kuma zai ɗaukaka shi zuwa ga zatinsa, nan da nan kuwa zai ɗaukaka shi. 33#Yah 7.34 Ya ku 'ya'yana ƙanana, saura ɗan lokaci kaɗan ina tare da ku. Za ku neme ni, amma kamar yadda na faɗa wa Yahudawa cewa, ‘Inda za ni ba za ku iya zuwa ba,’ haka nake faɗa muku yanzu. 34#Yah 15.12,17; 1Yah 3.23; 2Yah 1.5 Sabon umarni nake ba ku, shi ne ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, haka ku ma, ku ƙaunaci juna. 35Ta haka, kowa zai gane ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.”
Bitrus Zai Yi Musun Sanin Yesu
(Mat 26.31-35; Mar 14.27-31; Luk 22.31-34)
36Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ina za ka?” Yesu ya amsa ya ce, “Inda za ni, ba za ka iya bina yanzu ba, amma daga baya za ka bi ni.” 37Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, don me, ba zan iya binka a yanzu ba? Ai, zan ba da raina saboda kai.” 38Yesu ya amsa ya ce, “Ashe, za ka ba da ranka saboda ni? Lalle hakika, ina gaya maka, kafin zakara ya yi cara, za ka yi musun sanina sau uku.”

Sélection en cours:

Yah 13: HAU

Surbrillance

Partager

Copier

None

Tu souhaites voir tes moments forts enregistrés sur tous tes appareils? Inscris-toi ou connecte-toi