Logo YouVersion
Îcone de recherche

Yah 9

9
Warkar da Wanda aka Haifa Makaho
1Yesu na wucewa sai ya ga wani mutum da aka haifa makaho. 2Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, “Ya Shugaba, wa ya yi zunubi da aka haifi mutumin nan makaho, shi, ko iyayensa?” 3Yesu ya amsa ya ce, “Ba domin mutumin nan ko iyayensa sun yi zunubi ba, sai domin a nuna aikin Allah ne a kansa. 4Lalle ne mu yi aikin wanda ya aiko ni tun da sauran rana. Ai, dare zai yi sa'ad da ba mai iya aiki. 5#Mat 5.14; Yah 8.12 Muddin ina duniya ni ne hasken duniya.” 6Da ya faɗi haka sai ya tofa yau a ƙasa, ya cuɗa ƙasa, ya shafa a idanun makahon, 7ya ce masa, “Je ka, ka wanke ido a ruwan Siluwam,” wato aikakke. Shi ke nan sai ya je ya wanke ido, ya komo yana gani. 8Maƙwabta da waɗanda suka saba ganinsa dā yana bara, suka ce, “Ashe, ba wannan ne yakan zauna yana bara ba?” 9Waɗansu suka ce, “Shi ne mana.” Waɗansu kuwa suka ce, “A'a, kai dai, sun yi kama.” Shi kuwa ya ce, “Sosai ni ne!” 10Sai suka ce masa, “To, ƙaƙa aka yi idanunka suka buɗe?” 11Ya amsa ya ce, “Mutumin nan da ake kira Yesu ne ya cuɗa ƙasa ya shafa mini a idanu, ya ce mini, ‘Je ka Siluwam ka wanke ido.’ Na kuwa je na wanke, sai na sami gani.” 12Suka ce masa, “Ina yake?” Ya ce, “Ban sani ba.”
Farisiyawa Sun Bincika Labarin Wanda aka Warkar
13Sai suka kai wa Farisiyawa mutumin da yake makaho a dā. 14To, ran Asabar ne Yesu ya cuɗa ƙasar ya buɗe masa ido. 15Farisiyawa ma suka tambaye shi ta yadda aka yi ya sami gani. Ya ce musu, “Cuɗaɗɗiyar ƙasa ya shafa a idona, na wanke, ina gani.” 16Saboda haka, waɗansu Farisiyawa suka ce, “Mutumin nan ba daga Allah yake ba, don ba ya kiyaye Asabar.” Waɗansu kuwa suka ce, “Yaya mutum mai zunubi zai iya yin mu'ujizai haka?” Sai rabuwa ta shiga tsakaninsu. 17Sai suka sāke ce wa makahon, “To, kai fa, me ka gani game da shi, da yake kai ya buɗe wa ido?” Ya ce, “Ai, annabi ne.”
18Yahudawa kam, ba su gaskata shi makaho ne a dā ba, ya kuma sami gani, har suka kira iyayen wanda ya sami ganin, 19suka tambaye su suka ce, “Wannan ɗanku ne da kuke cewa an haife shi makaho? To, ta yaya yake iya gani yanzu?” 20Sai iyayen nasa suka amsa suka ce, “Mun dai san wannan ɗanmu ne, makaho ne aka haife shi. 21Amma ta yadda aka yi yake gani yanzu ba mu sani ba, ba mu ma san wanda ya buɗe idon ba. Ku tambaye shi, ai, ba yaro ba ne, zai faɗa da bakinsa.” 22Iyayensa sun faɗi haka ne don tsoron Yahudawa, don dā ma Yahudawa sun ƙulla, cewa kowa ya amsa, cewa shi ne Almasihu, za a fisshe shi daga jama'a. 23Shi ya sa iyayensa suka ce, “Ai, ba yaro ba ne, ku tambaye shi.”
24Sai suka sāke kiran mutumin nan da yake makaho a dā, suka ce masa, “Ka tsoraci Allah dai! Mu kam, mun san mutumin nan mai zunubi ne.” 25Sai ya amsa ya ce, “Ko mai zunubi ne, ni ban sani ba. Abu ɗaya kam, na sani, dā ni makaho ne, yanzu kuwa ina gani.” 26Sai suka ce masa, “Shin, me ya yi maka? Ta yaya ya buɗe maka ido?” 27Ya amsa musu ya ce, “Na riga na faɗa muku, ba ku ji ba. Don me kuke so ku sāke ji? Ko ku ma kuna so ku zama almajiransa ne?” 28Sai suka fāɗa shi da zagi, suna cewa, “Kai ne dai almajirin wannan ɗin, mu kam, almajiran Musa ne. 29Mun dai sani Allah ya yi magana da Musa, amma wannan ba mu san ta inda ya fito ba.” 30Sai mutumin ya amsa musu ya ce, “Yau ga abin mamaki! Ashe, ba ku san ta inda ya fito ba, ga shi kuwa, ya buɗe mini ido! 31Mun sani Allah ba ya sauraron masu zunubi, amma duk wanda yake mai bautar Allah, yake kuma aikata nufinsa, Allah yakan saurare shi. 32Tun da aka fara duniya ba a taɓa jin wani ya buɗe idon wanda aka haifa makaho ba. 33Da mutumin nan ba daga Allah ya fito ba, da ba abin da zai iya yi.” 34Suka amsa masa suka ce, “Kai da aka haifa a baƙin zunubi ne za ka koya mana?” Sai suka kore shi.
Makanta ta Ruhu
35Yesu ya ji labari sun kore shi. Da ya same shi, ya ce, “Ka gaskata da Ɗan Mutum ko?” 36Ya amsa ya ce, “Wane ne shi, ya Shugaba, da zan gaskata da shi?” 37Yesu ya ce masa, “Ai, ka gan shi, shi ne ma mai magana da kai.” 38Sai ya ce, “Ya Ubangiji, na ba da gaskiya,” ya kuma yi masa sujada. 39Yesu ya ce, “Na shigo duniyan nan ne don rarrabewa, domin waɗanda ba sa gani su gani, waɗanda suke gani kuma su makance.” 40Da Farisiyawan nan da suke tare da shi suka ji haka, suka ce masa, “Wato mu ma makafi ne?” 41Yesu ya ce musu, “Ai, da makafi ne ku, da ba ku da zunubi. Amma da yake kun ce kuna gani, to, zunubinku ya tabbata.

Sélection en cours:

Yah 9: HAU

Surbrillance

Partager

Copier

None

Tu souhaites voir tes moments forts enregistrés sur tous tes appareils? Inscris-toi ou connecte-toi