1
Luk 23:34
Littafi Mai Tsarki
Sai Yesu ya ce, “Ya Uba, ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa, suna kuri'a a kansu.
አወዳድር
{{ጥቅስ}} ያስሱ
2
Luk 23:43
Yesu ya ce masa, “Hakika, ina gaya maka, yau ma za ka kasance tare da ni a Firdausi.”
3
Luk 23:42
Ya kuma ce, “Ya Yesu, ka tuna da ni, sa'ad da ka shiga sarautarka.”
4
Luk 23:46
Sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Ya Uba, na sa ruhuna a ikonka.” Da ya faɗi haka kuwa, sai ya cika.
5
Luk 23:33
Da suka isa wurin da ake ce da shi Ƙoƙwan Kai, nan suka gicciye shi, da kuma masu laifin nan, ɗaya a damansa, ɗaya a hagun.
6
Luk 23:44-45
To, wajen tsakar rana ne kuwa, sai duhu ya rufe ƙasa duka, har zuwa ƙarfe uku na yamma. Hasken rana ya dushe. Labulen da yake cikin Haikali ya tsage gida biyu.
7
Luk 23:47
Sa'ad da jarumin ya ga abin da ya gudana, sai ya girmama Allah ya ce, “Hakika mutumin nan marar laifi ne!”
ቤት
መጽሐፍ ቅዱስ
እቅዶች
ቪዲዮዎች