Shi ya sa ban ga ma na isa in zo wurinka ba, amma kă yi magana kawai, yarona kuwa sai ya warke. Don ni ma a hannun wani nake, da kuma soja a hannuna, in ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai ya je, wani kuwa in ce masa, ‘Zo,’ sai ya zo, in ce wa bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai ya yi.” Da Yesu ya ji haka, ya yi mamakinsa, ya kuma juya ya ce wa taron da suke biye da shi, “Ina gaya muku, ko a cikin Isra'ila ban taɓa samun bangaskiya mai ƙarfi irin wannan ba.”