Farawa 24
24
Ishaku da Rebeka
1Yanzu fa Ibrahim ya tsufa, yana da shekaru masu yawa, Ubangiji kuma ya albarkace shi a kowace hanya. 2Sai Ibrahim ya ce wa babban bawan gidansa, wanda yake lura da duk abin da yake da shi, “Sa hannunka a ƙarƙashin cinyata. 3Ina so ka rantse da sunan Ubangiji Allah na sama da ƙasa, cewa ba za ka samo wa ɗana mata daga ’yan matan Kan’aniyawa, waɗanda nake zama cikinsu ba. 4Amma za ka tafi ƙasata da kuma cikin ’yan’uwana, ka samo mata saboda ɗana Ishaku.”
5Bawan ya ce masa, “Me zai faru in matar ba tă yarda tă zo tare da ni zuwa wannan ƙasa ba? In komar da ɗanka a ƙasar da ka fito ne ke nan?”
6Ibrahim ya ce, “Ka tabbata ba ka komar da ɗana can ba.” 7Ubangiji Allah na sama, wanda ya fitar da ni daga gidan mahaifina, da kuma ƙasar asalina wanda kuma ya yi magana da ni, ya yi mini alkawari da rantsuwa cewa, “Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa, zai aika mala’ikansa yă sha gabanka domin ka samo wa ɗana mata daga can. 8In matar ba tă yarda tă zo tare da kai ba, za a kuɓutar da kai daga wannan rantsuwa. Sai dai kada ka kai ɗana a can.” 9Saboda haka bawan ya sa hannunsa a ƙarƙashin cinyar maigidansa Ibrahim, ya kuma rantse masa game da wannan al’amari.
10Sai bawan ya ɗibi raƙuma goma na maigidansa ya tafi, ɗauke da kowane irin abubuwa masu kyau daga wurin maigidansa. Ya fita don yă tafi Aram-Naharayim, ya kama hanyarsa zuwa garin Nahor. 11Ya sa raƙuman suka durƙusa kusa da rijiya a bayan gari; wajen yamma ne, lokacin da mata sukan fita ɗiban ruwa.
12Sai ya yi addu’a ya ce, “Ya Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim, ka ba ni nasara yau, ka kuma nuna alheri ga maigidana Ibrahim. 13Duba, ina tsaye a bakin rijiyar ruwa, ’ya’ya matan mutanen gari kuma suna fitowa domin ɗiban ruwa. 14Bari yă zama sa’ad da na ce wa wata yarinya, ‘Ina roƙonki ki saukar da tulunki domin in sha,’ in ta ce, ‘Ka sha, zan kuma ba wa raƙumanka ma’; bari tă zama ita ce ka zaɓa wa bawanka Ishaku. Ta haka zan san cewa ka nuna wa maigidana alheri.”
15Kafin ya gama addu’a, sai Rebeka ta fito da tulu a kafaɗarta. Ita ’yar Betuwel ɗan Milka, matar Nahor, ɗan’uwan Ibrahim. 16Yarinyar kuwa kyakkyawa ce, budurwa, ba namijin da ya taɓa kwana da ita. Ta gangara zuwa rijiyar, ta cika tulunta ta kuma hauro.
17Bawan ya yi sauri ya same ta ya ce, “Ina roƙonki ki ba ni ɗan ruwa daga tulunki.”
18Ta ce, “Ka sha, ranka yă daɗe,” ta yi sauri ta saukar da tulun a hannuwanta, ta kuma ba shi, ya sha.
19Bayan ta ba shi ya sha, sai ta ce, “Zan ɗebo wa raƙumanka ruwa su ma, har sai sun gama sha.” 20Sai ta yi sauri ta juye ruwan da yake tulunta cikin kwami, ta koma zuwa rijiyar da gudu don ta ƙara ɗebo ruwa, ta kuma ɗebo isashe saboda dukan raƙumansa. 21Mutumin bai ce uffam ba, ya dai kalle ta sosai don yă san ko Ubangiji ya ba shi nasara a tafiyarsa ko babu.
22Sa’ad da raƙuman suka gama shan ruwa, mutumin ya fitar da zoben hanci na zinariya mai nauyin giram biyar da woroworo biyu na zinariya masu nauyin shekel goma, ya ba ta. 23Sa’an nan ya tambaye ta ya ce, “Ke ’yar wace ce? Ina roƙonki ki faɗa mini, akwai wuri a gidan mahaifinki da za mu kwana?”
24Sai ta ce masa, “Ni ’yar Betuwel ce ɗan da Milka ta haifa wa Nahor.” 25Ta ƙara da cewa, “Muna da isashen ciyawa da abincin dabbobi, da kuma wuri domin ku kwana.”
26Sa’an nan mutumin ya rusuna ya yi wa Ubangiji sujada, 27yana cewa, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim, wanda bai daina nuna alheri da amincinsa ga maigidana ba. Ni kam, Ubangiji ya bishe ni a tafiyata zuwa gidan ’yan’uwan maigidana.”
28Yariyan ta gudu ta faɗa wa mutanen gidan mahaifiyarta game da abubuwan nan. 29Rebeka fa tana da wani ɗan’uwa mai suna Laban, sai ya yi hanzari ya fita zuwa wurin mutumin a rijiyar. 30Nan da nan da ya ga zoben hancin da woroworo a hannuwan ’yar’uwansa, ya kuma ji Rebeka ta faɗa abin da mutumin ya ce mata, sai ya fita zuwa wurin mutumin, ya same shi yana tsaye wajen raƙuma kusa da rijiyar. 31Sai ya ce, “Zo, ya kai mai albarka na Ubangiji, don me kake tsaye a waje? Gama na shirya gida da wuri domin raƙuma.”
32Don haka mutumin ya tafi gidan, aka kuma saukar da kaya kan raƙuman. Aka kawo wa raƙuman ciyawa da abincin dabbobi, aka kuma kawo ruwa dominsa da mutanensa su wanke ƙafafunsu. 33Sa’an nan aka ajiye abinci a gabansa, amma ya ce, “Ba zan ci ba, sai na faɗi abin da yake tafe da ni.”
Sai Laban ya ce, “Faɗa mana.”
34Saboda haka ya ce, “Ni bawan Ibrahim ne. 35Ubangiji ya albarkaci maigidana sosai, ya kuma zama mai arziki. Ya ba shi tumaki, shanu, azurfa, zinariya, bayi maza da mata, raƙuma, da kuma jakuna. 36Saratu matar maigidana ta haifa masa ɗa a tsufanta, ya kuma ba shi duk mallakarsa. 37Maigidana ya sa na yi rantsuwa, ya kuma ce, ‘Kada ka ɗauko wa ɗana mata daga ’ya’ya matan Kan’aniyawa, waɗanda nake zama a ƙasarsu, 38amma ka tafi wajen gidan mahaifina da kuma dangina, ka ɗauko wa ɗana mata.’
39“Sai na ce wa maigidana, ‘A ce matar ba tă yarda tă zo tare da ni ba fa?’
40“Maigidana ya ce, ‘Ubangiji wanda yake tare da ni zai aiki mala’ikansa tare da kai, yă kuma sa tafiyarka tă yi nasara, don ka samo wa ɗana mata daga dangina, daga kuma gidan mahaifina. 41Ta haka za ka kuɓuta daga rantsuwata sa’ad da ka tafi wurin dangina, ko ma sun ƙi su ba ka ita, za ka kuɓuta daga rantsuwata.’
42“Sa’ad da na zo rijiya a yau, na ce, ‘Ya Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim, ina roƙonka ka ba ni nasara a tafiyar da na yi. 43Duba, ina tsaye kusa da wannan rijiya; in wata yarinya ta fito domin tă ɗiba ruwa, wadda in na ce mata, “Ina roƙonki bari in ɗan sha ruwa daga tulunki,” 44in ta ce, “Ka sha, zan kuma ba wa raƙumanka ma,” bari tă zama wadda Ubangiji ya zaɓar wa ɗan maigidana.’
45“Kafin in gama addu’ar, a zuciyata, sai ga Rebeka ta fito da tulunta a kafaɗarta. Ta gangara zuwa rijiyar ta ɗebo ruwa, na kuma ce mata, ‘Ina roƙonki ki ba ni ɗan ruwa daga tulunki.’
46“Ta yi sauri ta saukar da tulun daga kafaɗarta ta ce, ‘Sha, zan kuma ba wa raƙumanka su ma.’ Sai na sha, ta kuma shayar da raƙumana su ma.
47“Na tambaye ta, ‘Ke ’yar wane ne?’
“Ta ce, ‘’Yar Betuwel ɗan Nahor, wanda Milka ta haifa masa.’
“Sai na sa mata zobe a hancinta, woroworo kuma a hannuwata, 48na kuma sunkuya na yi wa Ubangiji sujada. Na yabi Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim wanda ya bi da ni a hanyar da take daidai, don in samo wa ɗan maigidana jikanyar ɗan’uwansa. 49Yanzu fa in za ku nuna wa maigidana alheri da aminci, ku faɗa mini, in kuma ba haka ba, ku faɗa mini, don in san hanyar da zan juya.”
50Laban da Betuwel suka ce, “Wannan daga wurin Ubangiji ne, ba abin da za mu ce I, ko a’a ba. 51Ga Rebeka, ɗauke ta ku tafi, bari tă zama matar ɗan maigidanka, yadda Ubangiji ya umarta.”
52Sa’ad da bawan Ibrahim ya ji abin da suka ce, sai ya rusuna har ƙasa a gaban Ubangiji. 53Sa’an nan bawan ya fito da kayan ado na zinariya da azurfa da kayayyaki na tufafi ya ba wa Rebeka; ya kuma ba wa ɗan’uwanta da mahaifiyarta kyautai masu tsada. 54Sa’an nan shi da mutanen da suke tare da shi suka ci, suka sha, suka kuma kwana a can.
Kashegari da safe da suka tashi sai ya ce, “A sallame ni in koma wurin maigidana.”
55Amma ɗan’uwanta da mahaifiyarta suka ce, “Bari yarinyar ta ɗan zauna tare da mu kwana goma ko fiye, sa’an nan ka#24.55 Ko kuwa ta ta fi.”
56Amma ya ce musu, “Kada ku tsai da ni, tun da Ubangiji ya ba ni nasara a tafiyata. Ku sallame ni domin in tafi wurin maigidana.”
57Sa’an nan suka ce, “Bari mu kira yarinyar mu tambaye ta game da zancen.” 58Saboda haka suka kira Rebeka suka ce mata, “Za ki tafi tare da mutumin nan?”
Sai ta ce, “Zan tafi.”
59Saboda haka suka sallame Rebeka, ’yar’uwarsu, duk da uwar goyonta da bawan Ibrahim da mutanensa. 60Suka kuma albarkaci Rebeka suka ce mata,
“’Yar’uwarmu, bari ki zama mahaifiyar
dubu dubbai,
bari zuriyarki su mallaki
ƙofofin abokan gābansu.”
61Sa’an nan Rebeka da bayinta mata suka shirya suka hau raƙumansu suka koma tare da mutumin. Da haka bawan ya ɗauki Rebeka ya tafi.
62Ishaku kuwa ya zo daga Beyer-Lahai-Royi, gama yana zama a Negeb. 63Wata rana da yamma ya fita zuwa fili domin yă yi tunani#24.63 Ma’anar Ibraniyanci na wannan kalma ba a tabbatar ba., sa’ad da ya ɗaga ido, sai ya ga raƙuma suna zuwa. 64Rebeka ma ta ɗaga ido sai ta ga Ishaku. Ta sauka daga raƙuminta da sauri, 65ta ce wa bawan, “Wane ne mutumin can a fili, da yake zuwa yă tarye mu?”
Bawan ya ce, “Maigidana ne.” Saboda haka ta ɗauki mayafinta to rufe kanta.
66Sai bawan ya faɗa wa Ishaku duk abin da ya yi. 67Ishaku ya kawo ta cikin tentin mahaifiyarsa Saratu, ya kuma auri Rebeka. Ta haka ta zama matarsa, ya kuwa ƙaunace ta; Ishaku kuma ya ta’azantu bayan rasuwar mahaifiyarsa.
Currently Selected:
Farawa 24: SRK
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.