Yohanna 8
8
1 Amma Yesu ya tafi Dutsen Zaitun.
2 Da sassafe ya sāke bayyana a filin haikali, inda dukan mutane suka taru kewaye da shi, sai ya zauna don yă koya musu. 3Sai malaman dokoki da Farisiyawa suka kawo wata macen da aka kama a zina. Suka sa ta tsaya a gaban taron 4suka kuma ce wa Yesu, “Malam, an kama wannan mace tana zina. 5A cikin Doka Musa ya umarce mu, mu jajjefe irin waɗannan mata. To, me ka ce?” 6Sun yi wannan tambaya ce don su sa masa tarko, don su sami hanyar zarge shi.
Amma Yesu ya sunkuya ya fara rubutu a ƙasa da yatsarsa. 7Da suka ci gaba da yin masa tambayoyi, sai ya miƙe tsaye ya ce musu, “In da wani a cikinku da ba shi da zunubi, sai yă fara jifanta da dutse.” 8Sai ya sāke sunkuyawa ya kuma yi rubutu a ƙasa.
9 Da jin haka, waɗanda suka ji sai suka fara tashi daga wurin ɗaya-ɗaya, tun daga babbansu har ya zuwa ƙaraminsu, sai da aka bar Yesu kaɗai, tare da macen tsaye a wurin. 10Sai Yesu ya miƙe tsaye ya tambaye ta ya ce, “Mace, ina suke? Ba wanda ya hukunta ki?”
11 Ta ce, “Ba kowa, ranka yă daɗe.”
Sai Yesu ya ce, “Haka ni ma ban hukunta ki ba. Ki tafi, ki daina rayuwar zunubi.”
Gaskiyar shaidar Yesu
12Sa’ad da Yesu ya sāke magana da mutanen, sai ya ce, “Ni ne hasken duniya. Duk wanda ya bi ni ba zai yi tafiya cikin duhu ba, sai dai yă sami hasken rayuwa.”
13Sai Farisiyawa suka tambaye shi suka ce, “Ga kai dai, kana yi wa kanka shaida, shaidarka kuwa ba tabbatacciya ba ce.”
14Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ko na shaidi kaina, ai, shaidata tabbatacciya ce, gama na san inda na fito da kuma inda za ni. Amma ku ba ku san inda na fito ko inda za ni ba. 15Kuna shari’a bisa ga ma’aunin mutane; ni kuwa ba na yin wa kowa shari’a. 16Amma ko da zan yi shari’a, shari’ata daidai ce, don ba ni kaɗai ba ne. Ina tare da Uba da ya aiko ni. 17A cikin Dokarku a rubuce yake cewa shaidar mutum biyu tabbatacciya ce. 18Ni ne nake shaidar kaina, Uba da ya aiko ni kuma yana shaidata.”
19Suka tambaye shi suka ce, “Ina Uban nan naka?”
Sai Yesu ya ce, “Ba ku san ni ko Ubana ba. Da kun san ni, da za ku san Ubana ma.” 20Ya faɗi waɗannan kalmomi ne yayinda yake koyarwa a filin haikali, kusa da inda ake ajiye baye-baye. Duk da haka ba wanda ya kama shi, domin lokacinsa bai yi ba tukuna.
21Har wa yau Yesu ya sāke ce musu, “Zan tafi, za ku kuwa neme ni, za ku kuma mutu cikin zunubinku. Inda za ni, ba za ku iya zuwa ba.”
22Wannan ya sa Yahudawa suka yi tambaya suka ce, “Zai kashe kansa ne? Shi ya sa yake cewa, ‘Inda za ni, ba za ku iya zuwa ba’?”
23Amma ya ci gaba da cewa, “Ku daga ƙasa kuke; ni kuwa daga bisa ne. Ku na duniyan nan ne; ni kuwa ba na duniyan nan ba ne. 24Na gaya muku cewa za ku mutu cikin zunubanku; in ba ku gaskata cewa ni ne wanda na ce nake ba, lalle za ku mutu cikin zunubanku.”
25Suka ce, “Wane ne kai?”
Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ni ne wannan da na sha faɗi muku. 26Ina da abubuwa masu yawa da zan faɗa game ku in kuma yi muku shari’a. Amma wanda ya aiko ni mai aminci ne, abin da kuma na ji daga gare shi, shi nake gaya wa duniya.”
27Ba su gane cewa yana yin musu magana game da Ubansa ba ne. 28Saboda haka Yesu ya ce, “Sa’ad da kuka ɗaga Ɗan Mutum, a sa’an nan ne za ku san cewa ni ne wannan da na ce nake. Ni kuwa ba na yin kome ni kaɗai, sai in dai faɗi abin da Uba ya koya mini. 29Wanda kuwa ya aiko ni yana tare da ni; bai bar ni ni kaɗai ba, domin kullum ina aikata abin da ya gamshe shi.” 30Sa’ad da yake cikin magana, da yawa suka ba da gaskiya gare shi.
’Ya’yan Ibrahim
31Sai Yesu ya ce wa Yahudawan da suka gaskata da shi, “In dai kun riƙe koyarwata, ku almajiraina ne da gaske. 32Sa’an nan za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za tă ’yantar da ku.”
33Sai suka amsa masa suka ce, “Ai, mu zuriyar Ibrahim ne kuma ba mu taɓa bauta wa kowa ba. Yaya za ka ce za a ’yantar da mu?”
34Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, duk mai yin zunubi bawan zunubi ne. 35Bawa dai ba shi da wurin zama na ɗinɗinɗin a cikin iyali, amma ɗa na gida ne har abada. 36Saboda haka in Ɗan ya ’yantar da ku, za ku ’yantu da gaske. 37Na dai san ku zuriyar Ibrahim ne. Duk da haka kuna shiri ku kashe ni, don maganata ba ta da wurin zama a cikinku. 38Ina faɗi muku abin da na gani a wurin Ubana, ku kuwa kuna yin abin da kuka ji daga wurin ubanku.”
39Suka ce, “To, ai, Ibrahim ne mahaifinmu.”
Yesu ya ce, “Da ku ’ya’yan Ibrahim ne, da za ku aikata abubuwan da Ibrahim ya yi. 40Ga shi kun ƙudura, sai kun kashe ni, ni mutumin da ya faɗa muku gaskiyar da na ji daga Allah. Ibrahim bai yi irin waɗannan abubuwa ba. 41Kuna yin abubuwan da ubanku yake yi ne.”
Suka ce, “Mu fa ba shegu ba ne. Uba guda kaɗai da muke da shi, shi ne Allah kansa.”
’Ya’yan Iblis
42Yesu ya ce musu, “Da Allah ne Ubanku, da kun ƙaunace ni, gama daga Allah na fito yanzu kuma ga ni nan. Ban zo saboda kaina ba, amma shi ne ya aiko ni. 43Me ya sa ba kwa gane da maganata? Don ba kwa iya jin abin da nake faɗi. 44Ku na ubanku ne, Iblis, kuna kuwa so ku aikata abin da ubanku yake so. Shi mai kisankai ne tun farko. Ba ruwansa da gaskiya, gama gaskiya ba ta cikinsa. Yayinda yake ƙarya, yana yin halinsa ne, gama shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma. 45Amma domin ina faɗin gaskiya, ba kwa gaskata! 46Akwai waninku da zai iya haƙaƙƙewa na taɓa yin zunubi? In kuwa gaskiya na faɗa, me ya sa ba kwa gaskata ni? 47Wanda yake na Allah, yakan ji abin da Allah yake faɗi. Abin da ya sa ba kwa jin sa kuwa shi ne don ku ba na Allah ba ne.”
Shaidar Yesu game da kansa
48Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Aha, ai, gaskiyarmu da muka ce kai mutumin Samariya ne, kana kuma da aljani.”
49Yesu ya ce, “Ni ba mai aljani ba ne, ni dai ina girmama Ubana, ku kuwa ba kwa girmama ni. 50Ba na nema wa kaina ɗaukaka, amma akwai wani wanda yake neman mini, shi ne kuma alƙali. 51Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya kiyaye maganata, ba zai ɗanɗana mutuwa ba sam.”
52Da jin haka Yahudawa suka ce, “Tabɗi, yanzu kam mun san kana da aljani! Ibrahim ya mutu haka ma annabawa, ga shi kana cewa duk wanda ya kiyaye maganarka ba zai ɗanɗana mutuwa ba sam. 53Ka fi Ibrahim mahaifinmu ne? Ya mutu, haka ma annabawa. Wa kake ɗauka kanka ne?”
54Yesu ya amsa ya ce, “In ma na ɗaukaka kaina, ɗaukakata ba kome ba ce. Ubana, wanda kuke cewa shi ne Allahnku, shi ne wanda yake ɗaukaka ni. 55Ko da yake ba ku san shi ba, ni dai na san shi. In kuwa na ce ban san shi ba, na zama maƙaryaci kamar ku ke nan, amma na san shi, kuma ina kiyaye maganarsa. 56Mahaifinku Ibrahim ya yi farin ciki sosai yă sami ganin ranata; ya kuwa gan ta, ya yi murna.”
57Sai Yahudawa suka ce masa, “Kai, shekarunka har yanzu ba su kai hamsin tukuna ba fa, har ka ga Ibrahim!”
58Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba, ni ne!” 59Da jin haka sai suka ɗebo duwatsu don su jajjefe shi, amma Yesu ya ɓuya, ya fita daga filin haikali.
Currently Selected:
Yohanna 8: SRK
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.