YouVersion Logo
Search Icon

Far 49

49
Faɗar Yakubu a kan 'Ya'yansa
1Yakubu ya kirawo 'ya'yansa maza, ya ce, “Ku tattaru wuri ɗaya don in faɗa muku abin da zai same ku a cikin kwanaki masu zuwa:
2“Ku taru ku ji, ya ku 'ya'yan
Yakubu, maza,
Ku kuma kasa kunne ga Isra'ila
mahaifinku.
3“Ra'ubainu, kai ɗan farina
ne, ƙarfina,
Ɗan balagata, isasshe kuma, mafi
ƙarfi duka cikin 'ya'yana.
4Kamar ambaliyar ruwa mai fushi
kake,
Amma ba za ka zama mafi daraja
ba,
Domin ka hau gadon mahaifinka,
Sa'an nan ka ƙazantar da shi.
5“Saminu da Lawi 'yan'uwa ne,
Suka mori takubansu cikin ta da
hankali.
6Ba zan shiga shawararsu ta asiri ba,
Ba kuwa zan sa hannu cikin taronsu
ba,
Gama cikin fushinsu suka kashe
mutane,
Cikin gangancinsu kuma suka
gurgunta bijimai.
7La'ananne ne fushinsu domin mai
tsanani ne,
Da hasalarsu kuma, gama bala'i ce.
Zan warwatsa su cikin dukan ƙasar
Yakubu,
In ɗaiɗaitar su su cikin Isra'ilawa.
8“Yahuza, 'yan'uwanka za su yabe ka,
Za ka shaƙe wuyan maƙiyanka,
'Yan'uwanka za su rusuna a gabanka.
9 # L.Ƙid 24.9; W.Yah 5.5 Yahuza ɗan zaki ne,
Ya kashe ganima sa'an nan ya komo
wurin ɓuyarsa.
Yahuza kamar zaki yake,
Yakan kwanta a miƙe,
Ba mai ƙarfin halin da zai tsokane shi.
10Yana riƙe da sandan mulkinsa,
Ya sa shi a tsakanin ƙafafunsa,
Har Shilo ya zo.
Zai mallaki dukan jama'o'i.
11Zai ɗaure aholakinsa a kurangar inabi,
A kuranga mafi kyau,
Zai wanke tufafinsa da ruwan inabi,
Ruwan inabi ja wur kamar jini.
12Idanunsa za su yi ja wur saboda shan ruwan inabi,
Haƙoransa kuma su yi fari fat
saboda shan madara.
13“Zabaluna zai zauna a gefen teku,
Zai zama tashar jiragen ruwa,
Kan iyakarsa kuma zai kai har
Sidon.
14“Issaka alfadari ne ƙaƙƙarfa,
Ya kwanta a miƙe tsakanin
jakunkunan shimfiɗa.
15Saboda ya ga wurin hutawa ne mai
kyau,
Ƙasar kuma mai kyau ce,
Sai ya sunkuyar da kafaɗunsa domin
ɗaukar kaya,
Ya zama bawa, yana yin aiki mai
wuya.
16“Dan zai zama mai mulki ga
mutanensa
Kamar ɗaya daga cikin kabilan
Isra'ila.
17Dan zai zama maciji a gefen hanya,
Zai zama kububuwa a gefen turba,
Mai saran diddigen doki
Don mahayin ya fāɗi da baya.
18Ina zuba ido ga cetonka, ya
Ubangiji.
19“Gad, 'yan fashi za su kai masa hari,
Shi kuwa zai runtume su.
20“Ashiru, ƙasarsa za ta ba da amfani
mai yawa,
Zai kuma yi tanadin abincin da ya
dace da sarki.
21“Naftali sakakkiyar barewa ce,
Mai haihuwar kyawawan 'ya'ya.
22“Yusufu jakin jeji ne,
Jakin jeji a gefen maɓuɓɓuga
Aholakan jeji a gefen tuddai.
23Maharba suka tasar masa ba tausayi
Suka fafare shi da kwari da baka.
24Duk da haka bakunansu sun
kakkarye.
Damatsansu sun yayyage
Ta wurin ikon Allah Mai Girma na
Yakubu,
Makiyayi, Dutse na Isra'ila.
25Ta wurin Allah na mahaifinka wanda
zai taimake ka,
Ta wurin Allah Mai Iko Dukka
wanda zai sa maka albarka
Albarkun ruwan sama daga bisa,
Da na zurfafa daga ƙarƙashin
ƙasa,
Da albarkun mama da na mahaifa.
26Albarkun hatsi da na gari
Albarkun daɗaɗɗun duwatsu,
Abubuwan jin daɗi na madawwaman
tuddai,
Allah ya sa su zauna a kan Yusufu,
Da a goshin wanda aka raba shi da
'yan'uwansa.
27“Biliyaminu kyarkeci ne mai kisa,
Da safe yakan cinye abin da ya
kaso,
Da maraice kuma yakan raba abin da
ya kamo.”
28Waɗannan duka su ne kabilan Isra'ila goma sha biyu, wannan kuma shi ne abin da mahaifinsu ya faɗa musu sa'ad da yake sa musu albarka. Ya sa wa kowannensu albarka da irin albarkar da ta cancance shi.
Rasuwar Yakubu da Jana'izarsa
29Yakubu ya umarce su, ya ce musu, “Ga shi, lokacin mutuwa ya gabato da za a kai ni wurin jama'ata da suka riga ni. Sai ku binne ni tare da kakannina a cikin kogon da yake a saurar Efron Bahitte, 30#Far 23.3-20 a cikin kogon da yake a Makfela, gabashin Mamre, a ƙasar Kan'ana, wanda Ibrahim ya saya duk da saurar, daga wurin Efron Bahitte, ya zama mallakarsa don makabarta. 31#Far 25.9,10; Far 35.29A can aka binne Ibrahim da Saratu matarsa. A can kuma suka binne Ishaku da Rifkatu matarsa. A can kuma na binne Lai'atu. 32Da saurar da kogon da yake cikinta, an saye su daga Hittiyawa.” 33#A.M 7.15 Sa'ad da Yakubu ya gama yi wa 'ya'yansa maza wasiyya, sai ya hau da ƙafafunsa bisa kan gado, Ya ja numfashinsa na ƙarshe, aka kuwa kai shi ga jama'arsa waɗanda suka riga shi.

Currently Selected:

Far 49: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in