Luk 5
5
An Kama Kifi Jingim
(Mat 4.18-22; Mar 1.16-20)
1 #
Mat 13.1,2; Mar 3.9,10; 4.1 Wata rana taro suna matsarsa domin su ji Maganar Allah, shi kuwa yana tsaye a bakin Tekun Janisarata, 2sai ya hangi ƙananan jirage biyu a bakin tekun, masuntan kuwa sun fita daga cikinsu, suna wankin tarunansu. 3Sai ya shiga ɗaya jirgin, wanda yake na Bitrus, ya roƙe shi ya ɗan zakuɗa da jirgin daga bakin gaci. Sai ya zauna ya yi ta koya wa taro masu yawa daga jirgin. 4Da ya gama magana, ya ce wa Bitrus, “Zakuɗa da jirgin zuwa wuri mai zurfi, ku saki tarunanku, ku janyo kifi.” 5#Yah 21.3 Bitrus ya amsa masa ya ce, “Ya Maigida, dare farai muna wahala, ba mu kama kome ba, amma tun da ka yi magana zan saki tarunan.” 6#Yah 21.6 Da suka yi haka kuwa, suka kamo kifi jingim, har ma tarunansu suka fara kecewa. 7Sai suka yafato abokan aikinsu a ɗaya jirgin su zo su taimake su. Suka kuwa zo, suka ciccika jiragen nan duka biyu kamar sa nutse. 8Da Bitrus ya ga haka, sai ya fāɗi a gaban Yesu ya ce. “Ya Ubangiji, wane ni da za ka tsaya kusa da ni, domin ni mutum ne mai zunubi.” 9Domin shi da waɗanda suke tare da shi duka, mamaki ya kama su saboda kifin nan da suka janyo, 10haka ma Yakubu da Yahaya 'ya'yan Zabadi, abokan sabgar Bitrus. Sai Yesu ya ce wa Bitrus, “Kada ka ji tsoro. Nan gaba mutane za ka riƙa kamowa.” 11Da suka kawo jiragensu gaci, suka bar kome duka suka bi shi.
Yesu Ya Warkar da Kuturu
(Mat 8.1-4; Mar 1.40-45)
12Wata rana Yesu na ɗaya daga cikin garuruwan nan, sai ga wani mutum wanda kuturta ta ci ƙarfinsa ya zo. Da ya ga Yesu ya fāɗi a gabansa, ya roƙe shi ya ce, “Ya Ubangiji, in dai ka yarda kana da ikon tsarkake ni.” 13Sai Yesu ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce, “Na yarda, ka tsarkaka.” Nan take sai kuturtar ta rabu da shi. 14#L.Fir 14.1-32 Yesu ya kwaɓe shi kada ya gaya wa kowa, ya ce, “Sai dai ka je wurin firist ya gan ka, ka kuma yi hadaya saboda tsarkakewarka, domin tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.” 15Amma duk da haka labarinsa sai ƙara yaɗuwa yake yi, har taro masu yawan gaske suka yi ta zuwa domin su saurare shi, a kuma warkar da su daga rashin lafiyarsu. 16Amma shi, sai ya riƙa keɓanta a wuraren da ba kowa, yana addu'a.
Yesu ya Warkar da Shanyayye
(Mat 9.1-8; Mar 2.1-12)
17Wata rana na koyarwa, waɗansu Farisiyawa kuwa da masanan Attaura da suka fito daga kowane gari na ƙasar Galili, da na ƙasar Yahudiya, daga kuma Urushalima, suna nan a zaune. Ikon Ubangiji na warkarwa kuwa yana nan. 18Sai ga waɗansu mutane ɗauke da wani shanyayye a kan shimfiɗa, suna ƙoƙari su shigar da shi su ajiye shi a gaban Yesu. 19Da suka kasa samun hanyar shigar da shi saboda taro, suka hau a kan soron, suka zura shi ta tsakanin rufin soron duk da shimfiɗarsa, suka ajiye shi a tsakiyar jama'a a gaban Yesu. 20Da Yesu ya ga bangaskiyarsu sai ya ce, “Malam, an gafarta maka zunubanka.” 21Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka fara wuswasi cewa, “Wane ne wannan da yake maganar saɓo? Wa yake iya gafarta zunubi banda Allah shi kaɗai?” 22Da Yesu ya gane wuswasinsu, ya amsa musu ya ce, “Don me kuke wuswasi haka a zuciyarku? 23Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi, ka yi tafiya’? 24Amma domin ku sakankance Ɗan Mutum na da ikon gafarta zunubi a duniya”, sai ya ce wa shanyayyen, “Na ce maka, tashi, ka ɗauki shimfiɗarka, ka tafi gida.” 25Nan take ya tashi a gaban idonsu, ya ɗauki abin kwanciyarsa, ya tafi gida, yana ɗaukaka Allah. 26Sai suka yi mamaki matuƙa, su duka, suka yi ta ɗaukaka Allah, tsoro kuma ya kama su, suka ce, “Yau mun ga al'ajabai!”
Kiran Lawi
(Mat 9.9-13; Mar 2.13-17)
27Bayan haka ya fita, ya ga wani mai karɓar haraji, mai suna Lawi, a zaune, yana aiki a wurin karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.” 28Sai ya bar kome duka, ya tashi ya bi shi.
29Sai Lawi ya yi masa ƙasaitacciyar liyafa a gidansa, akwai kuwa taron masu karɓar haraji da waɗansu mutane suna ci tare da su. 30#Luk 15.1,2 Sai Farisiyawa da malamansu na Attaura suka yi wa almajiransa gunaguni suka ce, “Don me kuke ci kuke sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?” 31Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da magani, sai dai marasa lafiya. 32Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai dai masu zunubi, su tuba.”
Tambaya a kan Azumi
(Mat 9.14-17; Mar 2.18-22)
33Sai suka ce masa, “Almajiran Yahaya suna azumi a kai a kai, suna kuma addu'a, haka kuma almajiran Farisiyawa, amma naka suna ci suna sha.” 34Sai Yesu ya ce musu, “Wato kwa iya sa abokan ango su yi azumi tun angon yana tare da su? 35Ai, lokaci na zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa'an nan ne fa za su yi azumi.” 36Ya kuma yi musu misali, ya ce, “Ba mai tsage ƙyalle a jikin sabuwar tufa ya yi maho a tsohuwar tufa da shi. In ma an yi, ai, sai ya kece sabuwar tufar, sabon ƙyallen kuma ba zai dace da tsohuwar tufar ba. 37Ba kuma mai ɗura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ma an ɗura, sai sabon ruwan inabin ya fasa salkunan, ya zube, salkunan kuma su lalace. 38Sabon ruwan inabi, ai, sai sababbin salkuna. 39Ba wanda zai so shan sabon ruwan inabin bayan ya sha tsohon, don ya ce, ‘Ai, tsohon yana da kyau.’ ”
Currently Selected:
Luk 5: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979