Yah 11

11
Mutuwar Li'azaru
1 # Luk 10.38,39 Wani mutum ne ya yi rashin lafiya, sunansa Li'azaru na Betanya, ƙauyen su Maryamu da 'yar'uwarta Marta. 2#Yah 12.3 Maryamun nan kuwa, wadda ɗan'uwanta Li'azaru ba shi da lafiya, ita ce wadda ta shafa wa Ubangiji man ƙanshi, ta kuma shafe ƙafafunsa da gashinta. 3To, 'yan'uwan nan mata suka aika masa, suka ce, “Ya Ubangiji, ga shi, wanda kake ƙaunan nan ba shi da lafiya.” 4Da Yesu ya ji haka ya ce, “Wannan rashin lafiya, ƙarshensa ba mutuwa ba ne, domin a ɗaukaka Allah ne, a kuma ɗaukaka Ɗan Allah ta wurinsa.”
5Yesu kuwa na ƙaunar Marta da 'yar'uwarta, da kuma Li'azaru. 6To, da ya ji Li'azaru ba shi da lafiya, sai ya ƙara kwana biyu. 7Bayan haka ya ce wa almajiran, “Mu koma ƙasar Yahudiya.” 8Almajiran suka ce masa, “Ya Shugaba, kwana kwanan nan fa Yahudawa suke neman jifanka, za ka sāke komawa can?” 9Yesu ya amsa ya ce, “Ba sa'a goma sha biyu ce yini ɗaya ba? Kowa yake tafiya da rana ba ya tuntuɓe, don yana ganin hasken duniyan nan. 10Amma kowa yake tafiya da dare yakan yi tuntuɓe, don ba haske a gare shi!” 11Ya faɗi haka, sa'an nan ya ƙara ce musu, “Amininmu Li'azaru ya yi barci, amma za ni in tashe shi.” 12Sai almajiran suka ce masa, “Ya Ubangiji, in dai barci ne ya ɗauke shi, ai, zai warke.” 13Alhali kuwa, Yesu zancen mutuwar Li'azaru yake, amma su sun ɗauka yana nufin barcin hutawa ne. 14Sai Yesu ya gaya musu a fili, ya ce, “Li'azaru dai ya mutu. 15Ina kuwa farin ciki da ba na nan, saboda ku domin ku ba da gaskiya. Amma mu dai je wurinsa.” 16Sai Toma, wanda ake kira Ɗan Tagwai, ya ce wa 'yan'uwansa almajirai, “Mu ma mu tafi, mu mutu tare da shi.”
Yesu Shi Ne Tashin Matattu da Rai Kuma
17Da Yesu ya isa, ya tarar Li'azaru, har ya kwana huɗu a kabari. 18Betanya kuwa kusa da Urushalima take, misalin mil biyu. 19Yahudawa da yawa sun zo su yi wa Marta da Maryamu ta'aziyyar ɗan'uwansu. 20Da jin Yesu na zuwa, sai Marta ta je taryensa, Maryamu kuwa ta zauna a gida. 21Sai Marta ta ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, da kana nan da ɗan'uwana bai mutu ba. 22Ko yanzu ma na sani kome ka roƙi Allah zai yi maka.” 23Yesu ya ce mata, “Ɗan'uwanki zai tashi.” 24Marta ta ce masa, “Na sani zai tashi a tashin matattu a ranar ƙarshe.” 25Yesu ya ce mata, “Ai, ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai. Wanda ya gaskata da ni, ko ya mutu zai rayu. 26Wanda kuwa yake raye, yake kuma gaskatawa da ni, ba zai mutu ba har abada. Kin gaskata wannan?” 27Ta ce masa, “I, ya Ubangiji. Na gaskata kai ne Almasihu, Ɗan Allah, shi wannan mai zuwa duniya.”
Yesu Ya Yi Hawaye
28Da ta faɗi haka, ta je ta kirawo 'yar'uwa tata Maryamu, ta raɗa mata ta ce, “Ga Malam ya zo, yana kiranki.” 29Ita kuwa da jin haka, ta yi maza ta tashi ta nufi wurinsa. 30Yesu dai bai iso ƙauyen ba tukuna, har yanzu yana wurin da Marta ta tarye shi. 31Da Yahudawan da suke tare da ita a cikin gida, suna yi mata ta'aziyya, suka ga Maryamu ta yi maza ta tashi ta fita, suka bi ta, suna zaton za ta kabarin ne, ta yi kuka a can. 32Da Maryamu ta iso inda Yesu yake, ta gan shi, sai ta faɗi a gabansa ta ce masa, “Ya Ubangiji, da kana nan da dan'uwana bai mutu ba.” 33Da Yesu ya ga tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita su ma, suna kuka, sai ya nisa a ransa, ya yi juyayi gaya. 34Ya kuma ce, “Ina kuka sa shi?” Suka ce masa, “Ya Ubangiji, zo ka gani.” 35Sai Yesu ya yi hawaye. 36Don haka Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake ƙaunarsa!” 37Amma waɗansunsu suka ce, “Ashe, wanda ya buɗe wa makahon nan ido, ba zai iya hana wannan mutum mutuwa ba?”
Yesu Ya Ta da Li'azaru daga Matattu
38Sai Yesu ya sāke nisawa a ransa, ya iso kabarin. Kabarin kuwa kogon dutse ne, da wani dutse kuma an rufe bakin. 39Yesu ya ce, “Ku kawar da dutsen.” Sai Marta, 'yar'uwar mamacin, ta ce masa, “Ya Ubangiji, ai, yanzu ya yi ɗoyi, don yau kwanansa huɗu ke nan da mutuwa.” 40Sai Yesu ya ce mata, “Ban gaya miki ba, in kin ba da gaskiya za ki ga ɗaukakar Allah?” 41Sai suka kawar da dutsen. Yesu kuwa ya ɗaga kai sama ya ce, “Ya Uba, na gode maka da ka saurare ni. 42Ko dā ma na sani koyaushe kana saurarona, amma na faɗi haka ne saboda jama'ar da suke nan tsaitsaye, domin su gaskata kai ne ka aiko ni.” 43Da ya faɗi haka ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Li'azaru fito!” 44Sai mamacin ya fito, ƙafa da hannu a ɗaure da likkafani, fuska tasa kuma a naɗe da mayani. Yesu ya ce musu, “Ku kwance masa, ya tafi.”
An Kulla Shawara Gāba da Yesu
(Mat 26.1-5; Mar 14.1-2; Luk 22.1-2)
45Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo wurin Maryamu, suka kuma ga abin da ya yi, suka gaskata da shi. 46Amma waɗansunsu suka tafi wurin Farisiyawa, suka gaya musu abin da Yesu ya yi. 47Don haka manyan firistoci da Farisiyawa suka tara 'yan majalisa, suka ce, “Shin, me muke yi ne, har mutumin nan yake ta yin mu'ujizai da yawa haka? 48In fa muka ƙyale shi kan haka, kowa zai gaskata da shi, Romawa kuma za su zo su karɓe ƙasarmu su ɗebe jama'armu.” 49Amma ɗayansu, wai shi Kayafa, wanda yake shi ne babban firist a shekaran nan, ya ce musu, “Ku dai ba ku san kome ba. 50Ba kwa lura, ai, ya fiye muku mutum ɗaya ya mutu saboda jama'a, da duk jama'a ta halaka.” 51Ba da nufinsa ya faɗi haka ba, sai dai da yake shi ne babban firist a shekaran nan, ya yi annabci cewa, Yesu zai mutu saboda jama'a, 52ba ma saboda jama'a kaɗai ba, har ma yă tattaro 'ya'yan Allah da suke warwatse ko'ina su zama ɗaya. 53Daga ran nan fa sai suka ƙulla su kashe shi.
54Saboda haka, Yesu bai ƙara tafiya a cikin Yahudawa a sarari ba, amma ya tashi daga wurin, ya tafi ƙasar da take a bakin jeji, ya shiga wani gari, mai suna Ifraimu. Nan ya zauna da almajiran.
55Ana nan, Idin Ƙetarewa na Yahudawa ya gabato, mutane da yawa daga ƙauye suka tafi Urushalima su tsarkake kansa kafin idin. 56Suka yi ta neman Yesu, suna tsaitsaye a Haikali, suna ce wa juna, “Me kuka gani? Zai zo idin kuwa?” 57Don dā ma, manyan firistoci da Farisiyawa sun yi umarni, cewa kowa ya san inda Yesu yake, ya zo ya faɗa, su kama shi.

S'ha seleccionat:

Yah 11: HAU

Subratllat

Comparteix

Copia

None

Vols que els teus subratllats es desin a tots els teus dispositius? Registra't o inicia sessió