Farawa 5

5
Daga Adamu zuwa Nuhu
1Wannan shi ne rubutaccen tarihin zuriyar Adamu.
Sa’ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin kamannin Allah. 2Ya halicce su namiji da ta mace, ya kuma albarkace su. Sa’ad da kuma aka halicce su, ya kira su “Mutum.”#5.2 Da Ibraniyanci adam
3Sa’ad da Adamu ya yi shekaru 130, sai ya haifi ɗa wanda ya yi kama da shi, ya kuma kira shi Set. 4Bayan an haifi Set, Adamu ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. 5Gaba ɗaya dai, Adamu ya yi shekaru 930, sa’an nan ya mutu.
6Sa’ad da Set ya yi shekara 105, sai ya haifi Enosh. 7Bayan ya haifi Enosh, Set ya yi shekara 807, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. 8Gaba ɗaya dai, Set ya yi shekaru 912, sa’an nan ya mutu.
9Sa’ad da Enosh ya yi shekara 90, sai ya haifi Kenan. 10Bayan ya haifi Kenan, Enosh ya yi shekara 815, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. 11Gaba ɗaya dai, Enosh ya yi shekaru 905, sa’an nan ya mutu.
12Sa’ad da Kenan ya yi shekara 70, sai ya haifi Mahalalel. 13Bayan ya haifi Mahalalel, Kenan ya yi shekara 840, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata 14Gaba ɗaya dai, Kenan ya yi shekara 910, sa’an nan ya mutu.
15Sa’ad da Mahalalel ya yi shekara 65, sai ya haifi Yared. 16Bayan ya haifi Yared, Mahalalel ya yi shekara 830, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata 17Gaba ɗaya dai, Mahalalel ya yi shekara 895, sa’an nan ya mutu.
18Sa’ad da Yared ya yi shekara 162, sai ya haifi Enok. 19Bayan ya haifi Enok, Yared ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. 20Gaba ɗaya dai, Yared ya yi shekara 962, sa’an nan ya mutu.
21Sa’ad da Enok ya yi shekara 65, sai ya haifi Metusela. 22Bayan ya haifi Metusela, Enok ya kasance cikin zumunci da Allah shekaru 300, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. 23Gaba ɗaya dai, Enok ya yi shekaru 365. 24Enok ya kasance cikin zumunci da Allah, sa’an nan ba a ƙara ganinsa ba. Saboda Allah ya ɗauke shi.
25Sa’ad da Metusela ya yi shekara 187, sai ya haifi Lamek. 26Bayan ya haifi Lamek, Metusela ya yi shekaru 782, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. 27Gaba ɗaya dai, Metusela ya yi shekaru 969, sa’an nan ya mutu.
28Sa’ad da Lamek ya yi shekara 182, sai ya haifi ɗa. 29Ya ba shi suna Nuhu#5.29 Nuhu ya yi kama da kalmar Ibraniyancin nan na ta’aziyya. ya kuma ce, “Zai yi mana ta’aziyya a cikin aikinmu da wahalar hannuwanmu a ƙasar da Ubangiji ya la’anta.” 30Bayan an haifi Nuhu, Lamek ya yi shekara 595, yana kuma da ’ya’ya maza da mata. 31Gaba ɗaya dai, Lamek ya yi shekaru 777, sa’an nan ya mutu.
32Bayan Nuhu ya yi shekara 500, sai ya haifi Shem, Ham da Yafet.

選択箇所:

Farawa 5: SRK

ハイライト

シェア

コピー

None

すべてのデバイスで、ハイライト箇所を保存したいですか? サインアップまたはサインインしてください。