1
Yohanna 14:27
Sabon Rai Don Kowa 2020
Salama na bari tare da ku; salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓaci kada kuma ku ji tsoro.
Mampitaha
Mikaroka Yohanna 14:27
2
Yohanna 14:6
Yesu ya amsa ya ce, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai dai ta wurina.
Mikaroka Yohanna 14:6
3
Yohanna 14:1
“Kada zuciyarku ta ɓaci. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni.
Mikaroka Yohanna 14:1
4
Yohanna 14:26
Amma Mai Taimako, Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba zai aiko cikin sunana, zai koya muku kome, zai kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku.
Mikaroka Yohanna 14:26
5
Yohanna 14:21
Duk wanda yake da umarnaina yana kuma yin biyayya da su, shi ne wanda yake ƙaunata. Wanda yake ƙaunata kuwa Ubana zai ƙaunace shi, ni ma zan ƙaunace shi, in kuma bayyana kaina gare shi.”
Mikaroka Yohanna 14:21
6
Yohanna 14:16-17
Zan kuwa roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimakon da zai kasance tare da ku har abada, Ruhun gaskiya. Duniya ba ta iya karɓarsa, don ba ta ganinsa ba ta kuma san shi ba. Amma kun san shi, saboda yana zama tare da ku zai kuma kasance a cikinku.
Mikaroka Yohanna 14:16-17
7
Yohanna 14:13-14
Kuma zan yi duk abin da kuka roƙa cikin sunana, don Ɗan ya kawo ɗaukaka ga Uban. Za ku iya roƙe ni kome a cikin sunana, zan kuwa yi.
Mikaroka Yohanna 14:13-14
8
Yohanna 14:15
“In kuna ƙaunata za ku yi biyayya da umarnina.
Mikaroka Yohanna 14:15
9
Yohanna 14:2
A cikin gidan Ubana akwai wurin zama da yawa; da a ce ba haka ba ne, da na gaya muku. Za ni can don in shirya muku wuri.
Mikaroka Yohanna 14:2
10
Yohanna 14:3
In kuwa na tafi na shirya muku wuri, sai in dawo in ɗauke ku ku kasance tare da ni don ku kasance inda nake.
Mikaroka Yohanna 14:3
11
Yohanna 14:5
Sai Toma ya ce masa, “Ubangiji, ba mu san inda za ka ba, to, ta yaya za mu san hanyar?”
Mikaroka Yohanna 14:5
Fidirana
Baiboly
Planina
Horonan-tsary