1
Yah 11:25-26
Littafi Mai Tsarki
Yesu ya ce mata, “Ai, ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai. Wanda ya gaskata da ni, ko ya mutu zai rayu. Wanda kuwa yake raye, yake kuma gaskatawa da ni, ba zai mutu ba har abada. Kin gaskata wannan?”
ႏွိုင္းယွဥ္
Yah 11:25-26ရွာေဖြေလ့လာလိုက္ပါ။
2
Yah 11:40
Sai Yesu ya ce mata, “Ban gaya miki ba, in kin ba da gaskiya za ki ga ɗaukakar Allah?”
Yah 11:40ရွာေဖြေလ့လာလိုက္ပါ။
3
Yah 11:35
Sai Yesu ya yi hawaye.
Yah 11:35ရွာေဖြေလ့လာလိုက္ပါ။
4
Yah 11:4
Da Yesu ya ji haka ya ce, “Wannan rashin lafiya, ƙarshensa ba mutuwa ba ne, domin a ɗaukaka Allah ne, a kuma ɗaukaka Ɗan Allah ta wurinsa.”
Yah 11:4ရွာေဖြေလ့လာလိုက္ပါ။
5
Yah 11:43-44
Da ya faɗi haka ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Li'azaru fito!” Sai mamacin ya fito, ƙafa da hannu a ɗaure da likkafani, fuska tasa kuma a naɗe da mayani. Yesu ya ce musu, “Ku kwance masa, ya tafi.”
Yah 11:43-44ရွာေဖြေလ့လာလိုက္ပါ။
6
Yah 11:38
Sai Yesu ya sāke nisawa a ransa, ya iso kabarin. Kabarin kuwa kogon dutse ne, da wani dutse kuma an rufe bakin.
Yah 11:38ရွာေဖြေလ့လာလိုက္ပါ။
7
Yah 11:11
Ya faɗi haka, sa'an nan ya ƙara ce musu, “Amininmu Li'azaru ya yi barci, amma za ni in tashe shi.”
Yah 11:11ရွာေဖြေလ့လာလိုက္ပါ။
ပင္မစာမ်က္ႏွာ
က်မ္းစာ
အစီအစဥ္
ဗီဒီယို