Farawa 10
10
Tsarin Al’ummai
1Wannan shi ne labarin Shem, Ham da Yafet, ’ya’yan Nuhu maza, waɗanda su ma sun haifi ’ya’ya maza bayan ambaliyar.
Mutanen Yafet
2’Ya’yan#10.2 ’Ya’ya maza na iya nufin zuriyoyi Ko kuwa magāda ko al’ummai; haka ma a ayoyi 3, 4, 6, 7, 20-23, 29 da 31. Yafet maza su ne,
Gomer, Magog, Madai da Yaban, Tubal, Meshek, da kuma Tiras.
3’Ya’yan Gomer maza su ne,
Ashkenaz, Rifat, da Togarma.
4’Ya’yan maza Yaban su ne,
Elisha, Tarshish, Kittim da Rodanim. 5(Daga waɗannan mutane ne masu zama a bakin teku suka bazu zuwa cikin ƙasashensu da kuma cikin al’ummansu, kowanne da yarensa.)
Mutanen Ham
6’Ya’yan Ham maza su ne,
Kush, Masar, Fut, da Kan’ana.
7’Ya’yan Kush maza su ne,
Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka.
’Ya’yan Ra’ama maza kuwa su ne,
Sheba da Dedan.
8Kush shi ne mahaifin Nimrod wanda ya yi girma ya zama jarumin yaƙi a duniya. 9Shi babban maharbi ne a gaban Ubangiji. Shi ya sa akan ce, kamar Nimrod babban maharbi a gaban Ubangiji. 10Cibiyoyin mulkinsa na farko su ne Babilon, Erek, Akkad, da Kalne a cikin Shinar. 11Daga wannan ƙasa, sai ya tafi Assuriya, inda ya gina Ninebe, Rehobot Ir, Kala 12da Resen, wadda take tsakanin Ninebe da Kala; wanda yake babban birni.
13Mizrayim shi ne mahaifin
Ludiyawa, Anamawa, Lehabiyawa, Naftuhiyawa, 14Fetrusiyawa, da Kasluhiyawa (inda Filistiyawa suka fito) da kuma Kaftorawa.
15Kan’ana shi ne mahaifin,
Sidon ɗan farinsa, da na Hittiyawa, 16Yebusiyawa, Amoriyawa, Girgashiyawa, 17Hiwiyawa, Arkiyawa, Siniyawa, 18Arbadiyawa, Zemarawa, da Hamawa.
Daga baya zuriyar Kan’aniyawa suka yaɗu 19har iyakar Kan’ana ta kai Sidon ta wajen Gerar har zuwa Gaza, sa’an nan ta milla zuwa Sodom, Gomorra, Adma da Zeboyim, har zuwa Lasha.
20Waɗannan su ne ’ya’yan Ham maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.
Mutanen Shem
21Aka kuma haifa wa Shem, wan Yafet, ’ya’ya maza. Shem shi ne kakan ’ya’yan Eber duka.
22’Ya’yan Shem maza su ne,
Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram.
23’Ya’yan Aram maza su ne,
Uz, Hul, Geter da Mash.
24Arfakshad ne mahaifin#10.24 Da Ibraniyanci; Seftuwajin, mahaifin shi ne Kainan, Kainan kuwa shi ne mahaifin Shela.
Shela kuma shi ne mahaifin Eber.
25Aka haifa wa Eber ’ya’ya maza biyu.
Aka ba wa ɗaya suna Feleg,#10.25 Feleg yana nufin rarrabuwa. gama a zamaninsa ne aka raba duniya; aka kuma sa wa ɗan’uwansa suna Yoktan.
26Yoktan shi ne mahaifin,
Almodad, Shelef, Hazarmawet, Yera, 27Hadoram, Uzal, Dikla, 28Obal, Abimayel, Sheba, 29Ofir, Hawila da Yobab. Dukan waɗannan ’ya’yan Yoktan maza ne.
30Yankin da suka zauna ya miƙe daga Mesha zuwa wajen Sefar a gabashin ƙasar tudu.
31Waɗannan su ne ’ya’yan Shem maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.
32Waɗannan su ne zuriyar ’ya’yan Nuhu maza bisa ga jerin zuriyarsu cikin al’ummominsu. Daga waɗannan ne al’ummomi suka bazu ko’ina a duniya bayan ambaliya.
Currently Selected:
Farawa 10: SRK
ማድመቅ
Share
Copy
ያደመቋቸው ምንባቦች በሁሉም መሣሪያዎችዎ ላይ እንዲቀመጡ ይፈልጋሉ? ይመዝገቡ ወይም ይግቡ
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.