Farawa 11
11
Hasumiyar Babilon
1To, a lokacin, yaren mutanen duniya ɗaya ne, maganarsu kuma ɗaya ce. 2Yayinda mutane suke ta yin ƙaura zuwa gabas, sai suka sami fili a Shinar, suka zauna a can.
3Suka ce wa juna, “Ku zo, mu yi tubula, mu gasa su sosai.” Suka yi amfani da tubula a maimakon duwatsu, kwalta kuma a maimakon laka. 4Sa’an nan suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni da hasumiyar da za tă kai har sammai, domin mu yi wa kanmu suna, don kada mu warwatsu ko’ina a doron ƙasa.”
5Sai Ubangiji ya sauko don yă ga birni da kuma hasumiyar da mutanen suke gini. 6Ubangiji ya ce, “Ga su, su jama’a ɗaya ce, su duka kuwa harshensu guda ne. Wannan kuwa masomi ne kawai na abin da za su iya yi, babu kuma abin da suka yi shirya yi da ba za su iya yi ba. 7Zo, mu sauka, mu rikitar da harshensu don kada su fahimci juna.”
8Saboda haka Ubangiji ya watsar da su daga wurin zuwa ko’ina a doron ƙasa, suka kuwa daina gina birnin. 9Shi ya sa aka kira birnin Babel,#11.9 Wato, Babilon; Babel ya yi kamar Ibraniyanci na rikitar. domin a can ne Ubangiji ya rikitar da harshen dukan duniya. Daga can Ubangiji ya watsar da su ko’ina a doron ƙasa.
Daga Shem zuwa Abram
10Wannan shi ne labarin Shem.
Shekara biyu bayan ambaliya, sa’ad da Shem ya yi shekara 100, sai ya haifi Arfakshad. 11Bayan ya haifi Arfakshad, Shem ya yi shekara 500, ya haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
12Sa’ad da Arfakshad ya yi shekara 35, sai ya haifi Shela. 13Bayan ya haifi Shela kuwa, Arfakshad ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.#11.12,13 Da Ibraniyanci; Seftuwajin (dubi kuma Luk 3.35,36 da kuma sharhi a Far 10.24) shekaru 35, ya haifi Kainan. 13 bayan kuma ya haifi Kaina, Arfakshad ya yi shekaru 430 ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata, sa’an nan ya mutu. Sa’ad da Kaina ya yi shekaru ɗari da talatin, ya haifi Shela. Bayan ya haifi Shela, Kaina ya yi shekaru 330 ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata
14Sa’ad da Shela ya yi shekaru 30, sai ya haifi Eber. 15Bayan ya haifi Eber, Shela ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
16Sa’ad da Eber ya yi shekaru 34, sai ya haifi Feleg. 17Bayan ya haifi Feleg, Eber ya yi shekara 430, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
18Sa’ad da Feleg ya yi shekaru 30, sai ya haifi Reyu. 19Bayan ya haifi Reyu, Feleg ya yi shekara 209, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
20Sa’ad da Reyu ya yi shekaru 32, sai ya haifi Serug. 21Bayan ya haifi Serug, Reyu ya yi shekara 207, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
22Sa’ad da Serug ya yi shekaru 30, sai ya haifi Nahor. 23Bayan ya haifi Nahor, Serug ya yi shekara 200, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
24Sa’ad da Nahor ya yi shekaru 29, sai ya haifi Tera. 25Bayan ya haifi Tera, Nahor ya yi shekara 119, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
26Bayan Tera ya yi shekaru 70, sai ya haifi Abram, Nahor da Haran.
27Wannan ita ce zuriyar Tera.
Tera ya haifi Abram, Nahor da Haran. Haran kuma ya haifi Lot. 28Yayinda mahaifinsa Tera yana da rai, Haran ya rasu a Ur ta Kaldiyawa, a ƙasar haihuwarsa. 29Abram da Nahor suka yi aure. Sunan matar Abram, Saira ne, sunan matar Nahor kuwa Milka; ita ’yar Haran ce, mahaifin Milka da Iska. 30Saira kuwa bakararriya ce, ba ta da yara.
31Tera ya ɗauki ɗansa Abraham, jikansa Lot ɗan Haran, da surukarsa Saira, matar Abram, tare kuwa suka bar Ur ta Kaldiyawa, don su tafi Kan’ana. Amma sa’ad da suka zo Haran sai suka zauna a can.
32Tera yi shekaru 205, ya kuma mutu a Haran.
Currently Selected:
Farawa 11: SRK
ማድመቅ
Share
Copy
ያደመቋቸው ምንባቦች በሁሉም መሣሪያዎችዎ ላይ እንዲቀመጡ ይፈልጋሉ? ይመዝገቡ ወይም ይግቡ
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.