Sa’an nan Yesu ya ɗauki burodin, ya yi godiya, ya kuma rarraba wa waɗanda suke zaune gwargwadon abin da ya ishe su. Haka kuma ya yi da kifin.
Sa’ad da duk suka ci suka ƙoshi, sai ya ce wa almajiransa,“Ku tattara gutsattsarin da suka rage. Kada kome yă lalace.”