Farawa Gabatarwa
Gabatarwa
Gabatarwa
Sunan nan Farawa ya fito daga kalmar Girik ce mai ma’ana “Masomi.” Wannan kuma shi ne littafin masomi, domin ya yi magana game da masomin duniya, masomin jinsin mutane, da kuma masomin mutanen Isra’ila.
Kashi na farko na Farawa (sura 1 zuwa sura 11) ya yi magana game da halitta da kuma jinsin mutane har zuwa lokacin Ibrahim. Kowane abin da Allah ya halitta, ya yi kyau. Sai dai mutum biyu na farko, wato, Adamu da Hawwa’u, sun yi rashin biyayya ga Allah, suka kuma shigar da mugu a cikin duniya. Mutane suka kasance masu zunubi ƙwarai, har Allah ya yanke shawara yă aika da ambaliyar ruwa don yă kashe kowa da kowa, sai dai wani mutum mai suna Nuhu tare da iyalinsa. Wannan mutum da iyalansa ne suka yi wa Allah sujada, saboda haka Allah ya ce musu su gina babban jirgin ruwa don su cece kansu da waɗansu dabbobi kaɗan daga kowace irin dabba da kowane irin tsuntsu. Bayan ambaliyar ruwan, sai mutane suka sāke yaɗuwa a duniya, yawancinsu kuwa suka daina yin wa Allah sujada.
Sauran littafin Farawa (sura 12 zuwa sura 50) ya ƙunshi labarin Abram da iyalinsa. Allah ya zaɓe su su kasance masomin mutanensa na musamman. Allah ya canja sunan Abram zuwa Ibrahim, da kuma sunan matar Abram, wato, Saira zuwa Saratu. Ibrahim da matarsa Saratu ba su da ’ya’ya amma Allah ya yi musu alkawari cewa za su haifi yaro kuma cewa zuriyarsu wata rana za tă kasance da ƙasarsu, su kuma zama albarka ga waɗansu al’ummai.
Ibrahim da Saratu suka tashi zuwa Kan’ana, ƙasar da Allah ya yi alkawari cewa zai ba wa zuriyarsu. Ibrahim da Saratu suka haifi ɗa, wanda suka ba shi suna Ishaku, a lokacin kuwa sun tsufa sosai. Ishaku daga baya ya haifi ’ya’ya biyu maza, wato, Yaƙub da Isuwa. Littafin ya kammala da labarin ’ya’yan Yaƙub maza goma sha biyu tare da iyalansu suna zama a Masar. Ɗaya daga cikin waɗannan ’ya’yan Yaƙub maza, mai suna Yusuf, ya zama gwamnar Masar. Yusuf fa ya san cewa wata rana Allah zai cika alkawarinsa ga mutanensa.
Currently Selected:
Farawa Gabatarwa: SRK
Tya elembo
Share
Copy
Olingi kobomba makomi na yo wapi otye elembo na baapareyi na yo nyonso? Kota to mpe Komisa nkombo
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.