1
Yohanna 4:24
Sabon Rai Don Kowa 2020
Allah ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa dole su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.”
Mampitaha
Mikaroka Yohanna 4:24
2
Yohanna 4:23
Duk da haka, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a Ruhu da kuma gaskiya, gama irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema.
Mikaroka Yohanna 4:23
3
Yohanna 4:14
amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba. Tabbatacce, ruwan da zan ba shi, zai zama masa maɓuɓɓugan ruwa da yake ɓuɓɓugowa har yă zuwa rai madawwami.”
Mikaroka Yohanna 4:14
4
Yohanna 4:10
Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah, da kuma wanda yake roƙonki ruwan sha, da kin roƙe shi, shi kuwa da ya ba ki ruwan rai.”
Mikaroka Yohanna 4:10
5
Yohanna 4:34
Yesu ya ce, “Abincina shi ne, in aikata nufin wannan da ya aiko ni, in kuma gama aikinsa.
Mikaroka Yohanna 4:34
6
Yohanna 4:11
Sai macen ta ce, “Ranka yă daɗe, ba ka da guga rijiyar kuwa tana da zurfi. Ina za ka sami wannan ruwan rai?
Mikaroka Yohanna 4:11
7
Yohanna 4:25-26
Macen ta ce, “Na san cewa Almasihu” (da ake ce da shi Kiristi) “yana zuwa. Sa’ad da ya zo kuwa, zai bayyana mana kome.” Sai Yesu ya ce, “Ni mai maganan nan da ke, Ni ne shi.”
Mikaroka Yohanna 4:25-26
8
Yohanna 4:29
“Ku zo, ku ga mutumin da ya gaya mini duk abin da na taɓa yi. Shin, ko shi ne Kiristi?”
Mikaroka Yohanna 4:29
Fidirana
Baiboly
Planina
Horonan-tsary